Babbar Magana: Sakateriyar Babban Birnin Tarayya Abuja Ta Kama da Wuta
- Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja, sun bayyana cewa wuta ta kama a sakateriyar tarayya dake Zone 3
- Jami'an hukumar kashe gobara sun shafe awannin suna aiki kafin daga ƙarshe su kashe wutar bayan amfani da motocin aikinsu hudu
- Wani shaidan gani da ido yace wasu mutum biyu sun jikkata kansu ta hanyar faɗowa daga hawa na biyu
Abuja - Wani ɓangare na sakateriyar babban birnin tarayya Abuja dake a Zone 3, cikin birnin Abuja ya kama da wuta yanzu haka, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Rahotanni dake fitowa yanzun haka sun tabbatar cewa babu wani cikakken bayani game da musabbabin kamawar wutar.
Hakanan kuma, gobarar ta shafi wasu daga cikin motocin dake harabar sakateriyar.
Legit.ng Hausa ta gano cewa jami'an hukumar kwana-kwana masu aikin kashe gobara na can na ƙoƙarin daƙile wutar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mutun biyu sun jikkata kansu
Wani shaidan gani da ido, ya shaidawa Channels tv cewa mutum sun yi tsalle sun diro daga hawa na biyu, inda wutar ta fara kamawa kuma sun jikkata kansu.
A cewar mutumin gobarar ta kama ne daga hawa na biyu na ginin farko a cikin sakateriyar, inda ya ƙunshi ma'aikatar ilimi ta ƙasa.
Shin an samu nasarar kashe wutar?
Jami'an hukumar kashe gobara sun kwashe tsawon awanni suna ƙoƙarin kashe wutar, kafin daga ƙarshe su samu nasarar kashe ta bayan kawo motocin aiki hudu.
Sakateriyar dake cikin birnin Abuja, ta ƙunshi manyan ma'aikatun gwamnati da sashi-sashi da kuma hukumomi na ƙasa.
A wani labarin kuma duba Hotunan yadda miyagun yan bindiga suka kai wani mummunan hari a jihar Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane da dama tare da ƙona gidaje da motoci.
Wannan hari na zuwa ne bayan gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai cikinsu harda katse sabis a jihar.
Asali: Legit.ng