Miji ya maka matarsa a kotu bisa ɗaukar cikin wani gardi duk da igiyar aurensa na kan ta

Miji ya maka matarsa a kotu bisa ɗaukar cikin wani gardi duk da igiyar aurensa na kan ta

  • Akinola Ikudola, mai shekaru 65 ya maka matar sa Funsho a kotu a ranar Alhamis
  • Hakan ya biyo bayan zargin ta da dauko cikin wani mutum daban da ta yi duk da igiyar auren sa na kan ta
  • Alkalin ya ce ya kamata a raba auren tunda ma’auratan sun gaji da zama da juna a matsayin miji da mata

Legas - Wata kotun gargajiya da ke jihar Legas, a ranar Alhamis, ta amince Akinola Ikudola dan kasuwa mai shekaru 65 ya rabu da matarsa Funsho bisa zargin ta da kunso ma sa cikin wani duk da igiyar auren sa na kan ta.

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye, ya ce ya kamata a raba auren tunda sun gaji da zama da juna a matsayin miji da mata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya yi iƙirarin wasu manya sun daƙo hayar masu kisa daga ƙasar waje su kashe shi

Miji ya maka matarsa a kotu bisa ɗaukar cikin wani gardi duk da igiyar aurensa na kan ta
Miji ya maka matarsa a kotu bisa ɗaukar cikin wani gardi duk da igiyar aurensa na kan ta. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito alkalin ya ce:

“Tunda duk kun gamsu da rabuwar auren, kotu ba ta da zabin da ya wuce ta raba auren.
“Don haka kotu ta raba auren da ke tsakanin Akinola da Funsho Ikudola yau.
“Daga yanzu kai da ita ba miji da mata bane.
“Ko wannen ku zai iya bin hanyar sa ba tare da cutar da wani ba; kotu tana muku fatan samun nasara a harkokin ku na rayuwa.”

Alkalin ya ba matar damar rike yaran su

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, alkali ya ba matar damar rike yaran su kuma ya bai wa Akinola umarnin biyan ta N10,000 duk wata don ciyar da su tare da wajabta ma sa ilimin yaran da walwalar su.

Koledoye ya umarci mai kara da ya biya N300,000 ga matar sa don ta nemi abin yi da rayuwar ta da kuma kudin haya.

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Kamar yadda alkalin ya ce:

“Mai kara zai biya N150,000 ga matar sa don ta nemi wani abin yi da rayuwar ta sannan ya kara wata N150,000 don ta biya haya tun da za ta bar gidan sa.”

Ikudola ya bukaci kotu ta raba auren su mai shekaru 21 sakamakon yadda matar sa ta dauko cikin wani mutum duk da igiyar auren sa da ke kan ta.

Kamar yadda ya bayyana wa kotu:

“Tun da ta sanar da ni tana da ciki na musanta batun ni ne uban yaron saboda babu wani abu da ya shiga tsakanin mu, amma na bar ta a gidan don in san wanene mai cikin.
“Lokacin da take nakuda, ta ki zuwa asibiti sai ta tsaya a gidan don ta haihu daga nan jaririn ya mutu.”
“Diyar mu ta farko da ba ta dade da kammala makarantar sakandare ba tana yawan kawo maza cikin gidan. Duk lokacin da na nemi matata ta tsawatar ma ta sai ta fara min fada.

Kara karanta wannan

Lars Vilks: Mutumin da ya yi zanen ɓatancin Annabi Muhammadu a Sweden ya mutu a hatsarin mota

“Funke ta bata damar zama da saurayin ta na tsawon watanni 3 ba tare da na sani ba, yanzu haka yarinyar ta na da ciki.”

Funsho ma ta ce mijin ta yana yawon barikin sa yadda yake so

Yayin da take mayar da martani, Funsho ta zargi mijin ta da yawon bariki. Kamar yadda matar ta bayyana:

“Kullum cikin yawo yake yi da mata iri-iri.”
Matar ta ce ta taba bai wa mijinta maganin da ya gusar masa da hankali sannan ta yi kwanciyar aure da shi saboda yadda yake tauye ma ta hakkin ta na tsawon shekaru 7.
“Miji na be damu da yaran mu ba da ni, yana yawan cewa yaran mu ba za su tuna da shi ba idan su ka daukaka nan gaba.”

Kuma ta bayyana cewa yaran sun lalace ne saboda yadda mahaifin su yake cutar da su.

Magidanci Ya Lakaɗa Wa Likitan Fata Mugun Duka Saboda Yaba Kyawun Fatar Matarsa

Kara karanta wannan

Boko Haram sun gurgunta mulki a Neja, sun kayyade shekarun aurar da 'ya'ya mata

A wani labarin daban, 'yan sanda sun kama wani mutum bayan ya lakada wa likita dukan tsiya inda ya bar shi a mawuyacin hali bayan yabon kyawun fatar matar sa.

Matar wacce musulma ce mai sanye da hijabi ta sanar da mijinta, Bakhriddin Azimov cewa likitan fatar dan asalin kasar Rasha, Vladimir Zhirnokleev ya yaba kyawun fatarta.

Daga nan ne mutumin ya kai wa likitan farmaki, yanzu haka yana fuskantar hukunci akan cin zarafi kamar yadda LIB ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164