Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas

Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas

  • Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi ya ce a bayyane ya ke akwai wadanda ke yakar yankin kudu maso gabas
  • Gwamnan ya zargi wasu Ndigbo da ke kasashen ketare da assasa rikicin da yankin ke fuskanta da kuma kashe-kashe
  • Ya ce ba za su yi biyayya ga IPOB ba wurin dokar zaman gida, saboda masu kafa dokar duk mayaudara ne da ke kasar waje

Abakaliki, Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, Dave Umahi, ya ce sun gano cewa an kaddamar da yaki kan yankinsu a yayin da ya ke martani kan kashe-kashen da 'yan bindiga ke wa jama'arsu.

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, Gwamna Umahi ya nuna damuwarsa da alhini kan kisan rayuka 12 da aka yi a yankin a makon da ya gabata kuma ya ce babu gaira balle dalili.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas
Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar tsaro na jihar a ofishin sabon gwamnan Abakaliki. Ya zargi wasu Ndigbo da ke zama a kasashen ketare da shirya rigingimun tare da daukar nauyinsu.

Gwamna Umahi ya umarci jama'ar yankin da su yi burus da umarnin zaman gida na 1 ga watan Oktoba tare da bada umarnin cewa a daga tutar Najeriya akasin umarnin IPOB, Leadership ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ana muzguna wa jama'ar Ebonyi sosai a baya tare da take musu hakkokinsu, an mayar da su yaran gida saboda dokar zaman gida kuma mun tashi domin gaggauta kamo sa'a.
"A don haka ba za mu cigaba da zaman gida ba. Hakazalika, duk wanda ya ce mu zauna a gida, jama'ar Ebonyi ba za su yi masa biyayya ba.
“Ina kira ga dukkan kudu maso gabas da su gane cewa wannan dokar zaman gidan da masu kafa ta 'yan uwan mu ne da ba su kasar nan kuma ake biyansu a kowacce sa'a.

Kara karanta wannan

Wike ya caccaki gwamnonin da suka dogara da kudaden shiga daga tarayya, ya ce babu wata jaha da ke a talauce

"Idan har da gaske su ke kuma suna son mu zauna a gida, dukkan jama'ar kudu maso gabas su dawo kasar nan.
"Duk ranar da suke son mu zauna gida, su zo mu zauna tare kuma mu ga ko za su iya komawa inda suka fito saboda hanyar samunsu ta toshe. Wannan abun duk yaudara ce," yace.

An siyasantar da diban ma'aikatan tsaro, Gwamna Zulum ya koka

A wani labari na daban, Gwamna Babagana Umara Zulun ba jihar Borno a ranar Laraba ya zargi daukan jami'an tsaro da hukumomin tsaron Najeriya ke yi aiki da saka siyasa a lamarin, abinda ke saka fannin tsaron kasar nan cikin mawuyacin hali.

Zulum na yin jawabi ne mai take 'Ungoverned Space and Insecurity in the Sahelian Region: Implications for Nigeria Domestic Peace and Security' a NIPSS da ke Kuru, jihar Filato, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya N20m ga duk wanda ke da bayanai kan kashe mijin Dora Akunyili

"Babbar matsala da ake samu wurin daukan aiki ne. Wadanda ake dauka aiki a rundunar sojin kasa, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro duk masu neman aiki ne. Da yawa daga cikinsu sun je wurin ne saboda ba su da aikin yi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel