Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba

Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba

- Garin Jalingo ya cika tankam da 'yan majalisar wakilai, sanatoci, 'yan majalisar jihar da dubban 'yan siyasa sakamakon jana'izar Mama Taraba

- Wurin karfe 5:15 gawarta ta sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Jalingo kuma an mika ta gidan mahaifinta dake GRA Jalingo

- Wurin karfe 6:46 na yammacin aka kai gawarta fadar sarkin Muri inda babban limami Nuru Dinga ya sallaceta tare da dubban jama'a

Jalingo, babban birnin jihar Taraba, ya cika tankam a ranar Litinin sakamakon jana'izar Hajiya AIsha Jummai Alhassan, tsohuwar ministan harkokin mata da walwalar yara, wacce aka fi sani da 'Mama Taraba'.

Gawarta ta isa filin sauka da tashin jiragen sama na Jalingo wurin karfe 5:15 na yamma kuma an kaita gidan mahaifinta dake kusa da gidanta a GRA Jalingo, Daily Trust ta ruwaito.

An kai gawar Jummai Alhassan fadar sarkin Muri wurin karfe 6:46 na dare kuma babban limamin Masallacin Jalingo, Imam Nuru Dinga ya ja dubban jama'a jana'izar.

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Onitsha bayan babbar mota dauke da harsasai ta fadi a titi

Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba
Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba. Hoto daga @daily_trust, @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Idin karamar sallah: Masarautar Kano za ta yi hawan daba

Jim kadan bayan kammala jana'izar, an dauka gawar Aisha zuwa makabartar Jeka da fari a motar asibiti kuma an birneta.

Jana'izar ta samu hallartar mataimakin gwamnan jihar Taraba, Haruna Manu, sanatoci, 'yan majalisar wakilai, 'yan majalisar jihar Taraba, sarakuna da dubban masu ta'aziyya.

Makabartar Jeka da fari ta cika da dubban 'yan siyasa da masu ta'aziyya daga ciki da wajen jihar Taraba.

Aisha Alhassan ta rasu tana da shekaru 61 kuma ta bar mahaifinta, 'ya'ya 3 da jikoki 13.

An haifeta a ranar Juma'a, tayi aure a ranar Juma'a kuma ta koma ga Allah ranar Juma'a.

Tun farko, Alhaji Isma'ila Yakawada ya jagoranci wakilai wadanda suka kaiwa Farfesa Ango Abdullahi gaisuwar ta'aziyya, tsohon mijinta da ta haifa 'ya'ya uku da shi.

A wani labari na daban, sakamakon zargin badakalar wasu kudade da ake yi kuma ya kai ga an dakatar da manajan daraktan hukumar kula da hanyoyin shige da fice na ruwan kasar nan (NPA) Hadiza Bala Usman, ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya kafa kwamitin mutum 11 domin bincikenta.

Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman ne sakamakon zarginta da ake da kalmashe wasu rarar kudi har N165 biliyan inda ta ki saka su a asusun gwamnati, zargin da ta musanta.

Kwamitin mutum 11 ya samu shugabancin Suleiman Auwalu, darakta ne a bangaren da ya shafi teku, sai Gabriel Fan, mataimakin darakta a bangaren shari'a, ma'aikatar sufuri ta tarayya ce zata yi aiki a matsayin sakatariyar kwamitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: