Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina

Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina

  • Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta yi fatali da bukatar Sanata Ndume na son zare kan shi daga tsaya wa Maina a kotu
  • Kamar yadda babbar kotun tace, ba ta da hurumin sauraron wannan bukata saboda akwai irin ta a gaban kotun daukaka kara
  • Idan za a tuna, Maina ya tsallake sharuddan beli inda ya tsere zuwa Nijar wanda hakan yasa kotu ta damke Sanata Ndume

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja a ranar Litinin ta yi watsi da bukatar da sanata Ali Ndume ya mika gabanta na son zare kan shi a matsayin tsayayyen Abdulrasheed Maina, bayan ya tsallake sharuddan beli.

Mai shari'a Okon Abang a hukuncin da ya yanke bayan bukatar da Ndume ya shigar gaban ta, ya ce hakan tamkar cin zarafin kotu ne ganin cewa ya mika irin wannan bukatar gaban kotun daukaka kara a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina
Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, ya tsallake beli bayan an sako shi daga gidan gyaran hali na Kuje inda ya kwashe kusan watanni 9 bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.

Ndume ne ya tsaya a matsayin tsayayyensa kuma ya karba belinsa bayan dan majalisar ya yi amfani da takardun wata kadararsa da za ta kai darajar naira miliyan dari biyar daga cikin sharuddan belin.

A hukuncinsa, Mai shari'a Abang, wanda yace ya duba bukatun dukkan bangaren, ya ce ba shi da hurumin sauraroron bukatar dan majalisa Ndume.

"A duk inda aka daukaka kara, kowacce bukata a gaban wannan kotun daukaka karar ya dace a mika ta.
"A don haka, duk wata bukata dacewa yayi a mika ta gaban kotun daukaka kara," ya yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Alkalin ya ce, duk da Maina wanda ya tsallake beli tare da tserewa an dawo da shi, hakan ba ya nufin kotun za ta iya sauraron bukatar Ndume.

Abang ya jaddada cewa, tunda batun janye belinsa da aka bada ya na hannun kotun daukaka kara, don haka ita za ta saurari korafin.

Kamar yadda yace, tunda daukaka karar har yanzu ba a saurara ba, ba shi da karfin ikon daukar mataki a kan abinda ke gaban kotun daukaka kara.

"A duk inda hakan ta faru, kotu ta na da karfin ikon fatali da hakan," yace.

A take kuwa alkali Abang ya yi watsi da wannan bukata.

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta karrama Muhammad Abu Ali, soja mai mukamin laftanal kanal kuma kwamandan bataliya ta 272 a baya wanda Boko Haram suka kashe a 2016.

Kara karanta wannan

Adamawa: Magidanci mai 'ya'ya 3 ya rasa ransa bayan shan guba da ya yi sakamakon rikici da matarsa

TheCable ta ruwaito cewa, a ranar 4 ga watan Nuwamban 2016, 'yan ta'addan Boko Haram sun halaka Ali yayin da suka kai wa bataliya ta 119 farmaki da ke Malam Fatori a jihar Borno.

Ali ya jagoranci daya daga cikin gagarumin artabun da sojin Najeriya suka yi da Boko Haram a watan Fabrairun 2015, wanda hakan yasa suka kwace garin Baga a Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng