Asiri ya tonu: Yan sanda sun damƙe gungun masu garkuwa dake aiki a gurin aje motoci a Kano

Asiri ya tonu: Yan sanda sun damƙe gungun masu garkuwa dake aiki a gurin aje motoci a Kano

  • Gwarazan jami'an yan sanda sun cafke wata tawagar masu garkuwa da mutane dake gudanar da aikinsu a tashoshin mota
  • Kakakin rundunar yan sanda ta ƙasa, Frank Mba, ya bayyana cewa jami'an sun kwato manyan makamai daga hannun mutanen
  • Ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga hannun, ya bayyana cewa yana ɗakko fasinja daga tashar mota domin garkuwa da su

Kano - Jami'an yan sanda sun cafke tawagar masu garkuwa da mutane da suka haɗa da maza 9 da mata biyu, waɗanda ke gudanar da aikinsu daga wurin aje motoci a cikin Kano, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Hakanan kuma gwarazan jami'an yan sandan sun damke mambobin wata ƙungiya da suka addabi mazauna yankin Gwagwalada, Kachia.

Da yake gabatar da mutanen da ake zargin a Abuja ranar Talata, kakakin rundunar yan sanda, yace jami'ai sun kwato bindigun AK-47 guda biyu, da sauran muggan makamai.

Kara karanta wannan

Zamu dandana musu zafin da mutane ke ji, Gwamna ya yi barazanar hukunta iyayen yan bindiga

Kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba
Asiri ya tonu: Yan sanda sun damƙe gungun masu garkuwa dake aiki a gurin aje motoci a Kano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ta ya suke gudanar da ayyukansu?

Daya daga cikin masu garkuwa da mutanen, Bashiru Sule yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina ɗaya daga cikin mambobin kungiyar masu garkuwa da mutane, shugabana ya faɗamun cewa garkuwa da mutane yana kawo kuɗi."
"Muna gudanar da ayyukan mu a Kano, sannan kuma mu ɗauki waɗanda muka sace zuwa cikin daji, inda shugaban mu yake jira."
"Wani lokacin na kan hawa mota a matsayin fasinja, wani lokacin kuma nine direba, ina ɗaukar fasinjoji kuma in baiwa yan tawagarmu labarin yawan mutanen da na ɗauko."

Kamar nawa kuke samu a garkuwa da mutane?

Sule ya ƙara da cewa a aikin da suka yi na ƙarshe, sun sace mutum uku kuma tawagarsu tana da sansanoni a manyan hanyoyin Jigawa, Kano, Kaduna da kuma Katsina.

"A aikin da muka gudanar na farko na samu dubu N70,000. A na biyu kuma na samu N40,000 da kuma dubu N30,000 a na ƙarshe."

Kara karanta wannan

Miyagun yan bindiga sun bude wa masallata wuta, Sun kashe aƙalla 10 a jihar Katsina

A wani labarin kuma Mutane Sun Shiga Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Hallaka Mutum 3 a Awka

An shiga tashin hankali a Awka, babban birnin jihar Anambra, biyo bayan hallaka mutum 3 da yan bindiga suka yi a birnin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Maharan sum bindige mutanen ne a kusa da kasuwa dake Ifite yayin da aka kashe mutum ɗaya a bayan asibitin koyarwa na ChukwuemekaɓOdumegwu Ojukwu, Amaku, ƙaramar hukumar Awka ta kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262