Gwamnatin Kano ta yi martani kan batun kame matar gwamna, Hajiya Hafsat Ganduje

Gwamnatin Kano ta yi martani kan batun kame matar gwamna, Hajiya Hafsat Ganduje

  • wamnatin jihar Kano ta yi martani kan batun kame matar gwamnan jihar Kano, Hajiya Hafsat Ganduje
  • Gwamnatin Kano ta ce, ba a kame ta ko tsare ta ba tana nan tana ci gaba da ayyukanta da suka dace
  • Gwamnatin ta kuma bayyana cewa, ya kamata mutane su ke gudun jita-jita da ake yadawa a kafafen sada zumunta

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da martani kan rahotannin da ke cewa hukumar EFCC ta cafke matar Gwamna Abdullahi Ganduje, Farfesa Hafsat Ganduje, tana mai cewa labarai ne kawai wadanda 'yan adawa ke daukar nauyin ta.

A cewar wata sanarwa, Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya nuna nadama kan jita-jitar, inda ya kara da cewa ba za a iya bin diddigin labarin da ba shi da tushe daga wata tushe mai kyauta ba kamar dai hukumar EFCC kanta.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari zai sake ciyo sabon bashin N6.258tr, Ministar Kudi

Gwamna Ganduja ya yi martani kan batun kame matar Goggo
Hafsat Ganduje a jirgi | Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa abin takaici, an yada labaran karya a kafafen sada zumunta ba tare da tabbatarwa daga gwamnati ko hukumar hana almundahanar ba, SaharaReporter ta ruwaito.

Garba ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba a kama matar gwamnan ko aka tsare ta ba kuma a halin yanzu tana nan tana sauke nauyin da ke kanta."

Kwamishinan ya yi kira ga mutanen kirki na jihar da su yi watsi da jita-jitar, inda ya bukace su da su kwantar da hankalinsu.

EFCC Ta Kama Matar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta kama, Haftsat Ganduje, matar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan zargin rashaswa da rikicin fili da dan ta ya yi karar ta, Premium Times ta ruwaito.

An kama ta ne makonni bayan ta ki amsa gayyatar da hukumar ta EFCC ta yi mata.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

Tunda farko dai EFCC ta gayyaci matar Gandujen zuwa hedkwatar ta a ranar 13 ga watan Satumba kamar yadda Premium Times ta ruwaito. Amma bata amsa gayyatar ba kuma EFCC ta yi barazanar kama ta.

Majiyoyi na kusa da ita daga baya sun bayyana cewa ta tafi Birtaniya ne domin hallartar bikin kammala karatun danta. Masu bincike na yi wa Haftsat Ganduje tambayoyi ne kan zargin da danta Abdulazeez Ganduje ya shigar a kanta.

Yadda kotu ta daure wani mutum shekaru 10 kan satar da abokinsa ya tafka

Wani matashi a kasar Ghana da aka fi sani da Kofi Sarfo ya ba da labarin wani abin bakin ciki da ya faru dashi kuma ya tilasta masa yin shekaru 10 masu kyau na rayuwarsa a gidan yari.

A cikin hirar da yayi da gidan talabijin na SV TV Africa, mutumin ya bayyana cewa yana can yana zaune lafiya wata rana abokinsa ya kawo kudi GHc3,600 (N244,442.97) don ya ajiye a dakinsa saboda suke kashewa kadan-kadan har su kare.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Kofi bai sani ba cewa an sato kudin ne daga hannun wani mutum, kuma tuni da ma ya dukufa don nemo wadanda suka masa barnar domin ya kamo su ya mika ga doka ta yi aikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel