Matukar ana son fatattakar APC a 2023, Wajibi jam'iyyar PDP ta yi abu daya, Shugaban Matasa
- Shugaban matasan PDP, Aliyu Bello, ya gargaɗi jam'iyyarsa kan kada ta yi kuskuren kai tikitin takarar shugaban ƙasa yanki ɗaya
- A cewarsa, kamata ya yi a bar kofa a buɗe ga duk wanda ke sha'awar tsayawa takara daga kowane yanki
- Bello yace yan Najeriya sun kosa PDP ta fitar da ɗan takarar da zai ceto su daga halin da APC ta jefa su
Kaduna - Shugaban matasan jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna, Aliyu Bello, yace matukar PDP tana son korar APC a zaɓen 2023, to wajibi ta baiwa kowa damar tsayawa takara, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Ya faɗi haka ne yayin da yake martani kan shawarar kwamitin karba-karba na PDP cewa kujerar shugaban jam'iyya a kaita yankin arewa.
Bello yace idan jam'iyyar PDP ta buɗe neman tikitin takarar shugaban ƙasa ga kowa, to zai magance matsalolin cikin gida da suka jawo faɗuwar jam'iyyar a 2015.
Kwamaret Bello, wanda shine shugaban ƙungiyar shugabannin matasa a yankin arewa ta yamma, yace gazawar APC wajen cika manyan alƙawurranta uku, shine damar PDP na sake ɗarewa karagar mulki, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Matakin da ya kamata PDP ta ɗauka
A jawabinsa, Bello yace:
"Muna kira ga uwar jam'iyya kada ta kai tikitin takarar shugaban ƙasa ga arewa ko kudu, kamata ya yi a bar dama ga kowane yankin Najeriya."
"Hakane zai bada damar yan takara daga kowane yanki su fafata, daga ƙarshe mu fitar da wanda ya fi dacewa ya ƙalubalanci APC."
Wace matsala karba-karba zai jawo wa PDP?
Shugaban matasan ya kuma yi gargaɗi cewa akwai sauran masu sauya sheka matukar jam'iyya ta ce dole sai ɗan yanki ɗaya zai nemi takara.
"Muna da yan takara daga Arewa da Kudu, waɗanda sun cancanci su gyara ƙasar nan. Saboda haka ina kira ga mambobin BoT, NEC da sauran masu faɗa a ji, su tabbatar da an bar kofa a buɗe ga kowa."
"Yan Najeriya sun ƙagu mu fitar da ɗan takarar da ya dace ya cece su daga hannun jam'iyyar APC."
A wani labarin kuma Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano
Rundunar yan sanda reshen jihar Kano, ta bayyana cewa ta damke mutum 7 da ake zargin suna da hannu a kisan wani malami a Kano.
Kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace mutanen sun ce, suna zargin shugaban CAN da ɓoye wani mai laifi.
Asali: Legit.ng