Yadda kotu ta daure wani mutum shekaru 10 kan satar da abokinsa ya tafka

Yadda kotu ta daure wani mutum shekaru 10 kan satar da abokinsa ya tafka

  • Wani mutum ya shafe shekaru 10 a gidan yari ta dalilin satar da abokinsa ya aikata ya lika masa
  • Bincike ne aka yi aka gano sauran kudin da abokinsa ya sato ya kawo dakinsa wannan yasa aka garkame shi
  • Rahoto ya bayyana yadda lamarin ya faru ta wata hira da aka yi dashi a gidan wani talabijin

Wani matashi a kasar Ghana da aka fi sani da Kofi Sarfo ya ba da labarin wani abin bakin ciki da ya faru dashi kuma ya tilasta masa yin shekaru 10 masu kyau na rayuwarsa a gidan yari.

A cikin hirar da yayi da gidan talabijin na SV TV Africa, mutumin ya bayyana cewa yana can yana zaune lafiya wata rana abokinsa ya kawo kudi GHc3,600 (N244,442.97) don ya ajiye a dakinsa saboda suke kashewa kadan-kadan har su kare.

Read also

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Yadda kotu ta daure wani mutum shekaru 10 kan satar da abokinsa ya tafka
Mutumin da aka daure shekaru 10 ta dalilin laifin abokinsa | Hoto: YouTube, SV TV Africa
Source: UGC

Kofi bai sani ba cewa an sato kudin ne daga hannun wani mutum, kuma tuni da ma ya dukufa don nemo wadanda suka masa barnar domin ya kamo su ya mika ga doka ta yi aikinta.

Yadda aka kamashi

A yawace-yawacensa, ainihin wanda ya aikata laifin ya sami labarin cewa mutumin yana kokarin kama shi kuma ya rufe shi kowa ya huta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai Kofi, wanda bai san abin da ke faruwa ba an bayyana shi a matsayin babban aminin barawon yayin bincike da nema a cikin dakinsa aka sami jakar barawon da sauran kudin a ciki.

Ana zuwa kotu, aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.

Kalli bidiyon hirar:

Martanin jama'a a kafar sada zumunta

Bobby Spurs ya nuna:

"Jami'in gwamnati na sace wa 'yan kasa bilyoyin biliyoyi .... 0 zero yrs a prison. Sahihancin siyasa hauka ne."

Read also

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

gilbert nkasia ya ce:

"Yawancin matasa suna lalata makomarsu da kaddararsu. Domin sun yi watsi da Yesu Kristi."

Bincike: Gida mai yawan mutum 4 na bukatar kashe N10k don dafa shinkafa jollof

A wani labarin, Talakawa ‘yan Najeriya na ci gaba da shan wahalar hauhawar farashin kayan abinci, inda tukunyar daya daga cikin shahararrun abincin kasar nan, shinkafa Jollof, yanzu za a iya kashe akalla Naira 10,00 don girkawa iyali mai mutane hudu.

Wannan ya karu da kashi 39.3% ko N2,913 akan N7,401 da ake kashewa a watan Janairun 2017 don shirya irin wannan abinci.

An samar da wannan kima ne yayin da aka kimanta nazarin matsakaicin farashin kayan masarufi da ya fito daga Ofishin Kididdiga na Kasa ta a watan Agusta 2021 wanda aka zaba cikin rahoton farashin abinci da aka fitar ranar Talata, 21 ga Satumba, 2021.

Source: Legit.ng

Online view pixel