Bincike: Gida mai yawan mutum 4 na bukatar kashe N10k don dafa shinkafa jollof

Bincike: Gida mai yawan mutum 4 na bukatar kashe N10k don dafa shinkafa jollof

Bincike ya bayyana cewa, ana bukatar makudan kudaden da suka haura N10,000 don girka shinkafa jollof da mutane hudu za su ci. Wannan yasa wani bincike da NBS ta gudanar ya fitar bayanin yadda kayayyaki suka tashi a Najeriya.

Talakawa ‘yan Najeriya na ci gaba da shan wahalar hauhawar farashin kayan abinci, inda tukunyar daya daga cikin shahararrun abincin kasar nan, shinkafa Jollof, yanzu za a iya kashe akalla Naira 10,00 don girkawa iyali mai mutane hudu.

Wannan ya karu da kashi 39.3% ko N2,913 akan N7,401 da ake kashewa a watan Janairun 2017 don shirya irin wannan abinci.

An samar da wannan kima ne yayin da aka kimanta nazarin matsakaicin farashin kayan masarufi da ya fito daga Ofishin Kididdiga na Kasa ta a watan Agusta 2021 wanda aka zaba cikin rahoton farashin abinci da aka fitar ranar Talata, 21 ga Satumba, 2021.

Read also

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

Bincike: Gida mai yawan mutum 4 na bukatar kashe N10k don dafa shinkafa jollof
Shinkafa Jollof | Hoto: thedinnerbite.com
Source: UGC

Wadannan sinadaran sun hada da hadin shinkafa, tumatir, albasa, man girki, nama, kaza da naman sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dangane da bayanan NBS, kowanne daga cikin abubuwan da aka ambata farashinsu a kilo I ya karu akalla da 30% a cikin shekaru hudu da suka gabata.

Shinkafa

Misali, kilo daya na shinkafar gida da ake sayarwa N286.19 a watan Janairun 2017 an koma sayar da ita akan N409.97 a watan Agusta 2021.

Farashin shinkafa da aka shigo da ita ya kuma karu a watan Agusta zuwa N546.71 daga N402.01 da aka sayar da ita a farkon shekarar 2017.

Tumatir

Tumatir, wani muhimmin sinadarin abinci ya tashin gwauron zabi sosai zuwa N396.38 daga N247.55 da aka sayar a shekarar 2017.

Albasa

Albasa albasa muhimmin kayan abinci mai karin dandano a Jollof shima ya karu daga N258.92 zuwa N302.88.

Read also

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Man gyada

Iyalan da ke amfani da man gyada za su bukaci biyan N769.45 a kwalba idan aka kwatanta da N495.29 da aka sayar a shekarar 2017.

Kaza

Kafa da fuka-fukin kaji sun tashi daga N768.11 da N886.58 shekaru hudu da suka gabata zuwa N819.03 da N1080.13 bi da bi a watan Agusta 2021.

Kilo daya na daskararriyar kaza kuma ya tashi zuwa N2,091.34 a watan Agusta daga N1,419.75 da aka sayar a watan Janairun 2017.

Idan aka tara alkaluman kowanne daga cikin kayayyakin nan, zai kama akalla N10,000.

A cikin irin wannan bincike, wanda SBM Intelligence wani kamfanin bincike ya gudanar, a karshen watan Yuni, matsakaicin farashin girka tukunyar shinkafa jollof ya tashi zuwa N7,618.

Kamfanin da yayi nazari kan farashin kayan abinci a kasuwannin Onitsha, Fatakwal da Calabar ya ce farashin naman sa, albasa da manyan abubuwan tumatir duk sun karu saboda hauhawar rashin tsaro.

Read also

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Nama ya kare a jihar Kwara sakamakon tsadar farashin shanu a yankin

A bangare guda, Rahoto daga Daily Trust ya ce, mahauta a jihar Kwara sun daina yanka shanu sakamakon tsadar kayan masarufi.

Wannan lamarin ya haifar da karancin nama a duk kasuwanni a Ilorin, babban birnin jihar.

Wani mahauci a Kasuwar Mandate da aka fi sani da Alfa ya ce ba za su iya samun naman da za su saya daga dukkan mahautan da ke Ilorin ba.

Source: Legit.ng

Online view pixel