Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

  • Sanata Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya ce ba ya cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa
  • Kamar yadda gwamnan yace yayin addu'ar cikarsa shekaru sittin da uku a duniya, ya ce tabbas mulki na Allah ne
  • Gwamnan ya ce dole ne ya yi godiya ga Allah saboda ya yi darakta, sanata, minista kuma gwamna bayan fitowa daga gidan sarauta

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya ce ba ya cikin matsananciyar bukatar fitowa takarar kujerar shugabancin kasa saboda mulki dai Allah ne ke badawa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Ya kara da cewa, ya zabi ya yi addu'a ta musamman domin murnar cikarsa shekaru sittin da uku a duniya sakamakon baiwa mara misaltuwa da Allah ya yi masa ballantana a bangaren shugabancin.

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi
Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron addu'a ta musamman da aka yi a gidan gwamnatin jihar ranar Talata a garin Bauchi domin murnar cikarsa shekaru sittin da uku a duniya.

Read also

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gwamnan ya ce:

"Na fito daga gidan sarauta, na zama darakta, na zama sanata, na rike mukamin minista kuma yanzu ga ni a matsayin gwamna. Babu mukamin da ban rike ba. Dole ne in mika godiyata ga Allah da dukkanku kan goyon bayana da ilhama.
"Har ila yau, a kan kiran da ake ta min domin in yi takarar shugabancin kasa, zai yuwu saboda yadda na bada gudumawa mai tarin yawa ne wurin habakar jihar Bauchi.
“Ina alfahari da abinda na zama. Na san akwai wasu gibi a nan da can a bangaren shugabanci da tallafawa da sauransu.
"Duk idan ka samu kan ka a shugabanci, ka gode wa Ubangiji da ya gwada ka saboda shugabancin nauyi ne babba," yace.

Read also

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Kotu ta yi fatali da bukatar Ndume ta zare hannunsa daga shari'ar Maina

A wani labari na daban, Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja a ranar Litinin ta yi watsi da bukatar da sanata Ali Ndume ya mika gabanta na son zare kan shi a matsayin tsayayyen Abdulrasheed Maina, bayan ya tsallake sharuddan beli.

Mai shari'a Okon Abang a hukuncin da ya yanke bayan bukatar da Ndume ya shigar gaban ta, ya ce hakan tamkar cin zarafin kotu ne ganin cewa ya mika irin wannan bukatar gaban kotun daukaka kara a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Maina, tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, ya tsallake beli bayan an sako shi daga gidan gyaran hali na Kuje inda ya kwashe kusan watanni 9 bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel