2023: Ai ba a yin dole a siyasa – Tsohon Gwamnan Arewa ya yi wa Gwamnonin Kudu raddi
- Sule Lamido ya yi tir da matsayar da gwamnonin Kudancin Najeriya suka dauka
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa ya fada wa gwamnonin cewa ba a yin dole a siyasa
- ‘Dan siyasar yake cewa ba za a kai mulki Kudu saboda san ran wasu gwamnoni ba
Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya maida martani a kan matsayar gwamnonin Kudu a game da zaben shugaban kasa na 2023.
A wata hira da BBC Hausa tayi da shi, wanda aka wallafa a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, 2021, ya bayyana abin da ya kamata ayi wajen fito da shugabanni.
Alhaji Sule Lamido ya soki salon da gwamnonin jam’iyyar APC da PDP na kudancin Najeriya suka dauka na cewa ya zama wajibi a mika wa 'Yan Kudu mulki.
Babban jigon na jam'iyyar adawa ta PDP a Arewacin Najeriya yace ba a yin dole a siyasa, domin kowa ‘da ne, kuma yana da hakki a siyasance da jam’iyyance.
Sule Lamido ya yi magana
“’Yan Kudu na PDP da APC sun taru, sun kwatsa, sun zama abu daya, suna cewa dole sai an ba su mulki. Ai babu maganar dole a siyasa, kowa ‘da ne, kowa mai ‘yanci ne.”
Babban ‘dan adawar ya shaida wa BBC cewa muddin aka koma bangaranci, an sauka daga siyasa. Sule ya ja-kunnen shugabanni su rika tuna kalaman da za suyi.
“Idan ka ce kai sai naka, nima ai akwai nawa kenan. Wajen kalamai ya kamata a maida hankali da basira. Ka da ayi abin da zai kawo zolaya.”
Ba yau aka fara ba - Sule
“Jam’iyyar PDP ta ‘Yan Najeriya ce, kowa ‘da ne, kuma yana da ‘yanci. Kuma muna yi ne domin kasa ba wani bangare ba. Mun saba yin abu domin kasa."
-Sule Lamido
Sule Lamido yace akwai lokacin da aka zakulo ‘dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu, kuma duk ‘Yan Arewa suka hakura ba don an fi karfinsu ba.
“Ai an taba yin haka shekaru da suka wuce, aka dauko Obasanjo aka ce shi zai yi takara, amma ka ga ai ba dole ta sa aka yi wannan ba, ganin kasar ne da yanayinta."
CNG ba ta tare da Gwamnonin Kudu
Dazu aka ji cewa gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya, ta nuna adawarta ga tsarin karba-karba da jam’iyyun siyasa suke kawo wa yayin da ake shirin 2023.
Mai magana da yawun bakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman, ya bayyana cewa wannan tsaro ya saba dokar kasa, kuma yunkuri ne na murkushe ‘yan siyasan Arewa.
Asali: Legit.ng