'Yan ta'addan IPOB sun kona gidan hadimin gwamnan jihar Legas

'Yan ta'addan IPOB sun kona gidan hadimin gwamnan jihar Legas

  • 'Yan ta'addan IPOB sun bankawa gidan wani hadimin gwamnan jihar Legas wuta a garinsu
  • Hadimin gwamnan dan asalin jihar Anambra ne amma mazaunin Legas kuma gidan nasa na Nnewi ta jihar Anambra
  • Ya bayyana yadda gidan nasa ke ci da wuta yayin da kyamerar CCTV ta dauki lokacin da ake kone gidan

Anambra - Wasu tsageru da ba a san ko su waye ba sun kai hari gidan Joe Igbokwe, mai taimakawa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a Nnewi, jihar Anambra.

Hakazalika an kona gidan jigon na jam'iyyar APC a ranar Lahadi da yamma, 3 ga watan Oktoba, inji rahoton Sahara Reporters.

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kona gidan hadimin gwamnan jihar Legas
Yayin da aka kone gidan hadimin gwamna | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

IPOB ce ke da alhakin kai harin

Igbokwe wanda ke zaune a jihar Legas ya zargi 'yan ta'adda masu fafutukar a ware na kafa kasar Biafra wato IPOB da alhakin kai harin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An yi wa jami'in DSS kisar gilla a jihar Imo

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wani sakon da ya wallafa a Facebook, ya lura cewa kyamarorin CCTV sun nadi kone-kone yayin da suke isa cikin abin hawa a gidansa.

Rubutun ya ce::

"Gashi nan. An sadaukar da Gida na a Nnewi. Ba a rasa rai ba. Daukaka ta tabbata ga Allah.
“IPOB sun mamaye gidana da ke Nnewi kusan yanzu. Na tabbata sun tunkari gidana suna dauke da jarkokin man fetur da na gani ana sauke su daga mota kirar Sienna ta CCTV. Daukaka ta tabbata ga Allah. Har yanzu ina raye.”

Guardian ta yada wani bidiyo a kafar Facebook wanda ke nuna gidan Igbokwe bayan an kone shi.

'Yan bindiga sun kai hari asibiti, sun bankawa motar hukumar DSS wuta

A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ke tafe a cikin motocin SUVs guda hudu a yau Lahadi sun kashe mutane biyu yayin wani hari a garin Nnewi mai yawan masana'antu a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

2023: Ai ba a yin dole a siyasa – Tsohon Gwamnan Arewa ya yi wa Gwamnonin Kudu raddi

Sun kuma bankawa daya daga cikin motoci mallakar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) wuta.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa 'yan bindigan sun kai harin ne a daidai lokacin da masu ibada ke kammala hidimarsu cocinsu daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel