Matsalar tsaron da yankin Arewa ke fama da shi Abun damuwa ne matuka, Sarkin Zazzau

Matsalar tsaron da yankin Arewa ke fama da shi Abun damuwa ne matuka, Sarkin Zazzau

  • Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Bamalli, ya nuna damuwarsa game da halin matsalar tsaro da yankin Arewa ke ciki
  • Sarkin yace ya zama wajibi yan Najeriya su cigaba da tallafawa kokarin gwamnati na kawo ƙarshen matsalar
  • Bamalli ya yi godiya ga Allah (SWT) da ya ba shi ikon zama sarkin Zazzau, ba don wani karfi ko dabararsa ba

Zaria - Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara mamaye Arewa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Sarkin ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su tallafawa gwamnatin tarayya a kokarin da take na kawo karshen matsalolin tsaro a faɗin ƙasa.

Bamalli, wanda ya nuna cancantar mahaifinsa ya zama sarki fiye da shi, ya yi kira ga masu hannu a matsalar tsaro da yan bindiga su tuba, domin kawo zaman Lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli
Matsalar tsaron da yankin Arewa ke fama da shi Abun damuwa ne matuka, Sarkin Zazzau Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Sarkin ya yi wannan furuci ne a wata hira da sashin Hausa na BBC, ana gab da bikin cikarsa shekara ɗaya da zama Sarkin Zazzau.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene fatan sarkin Zazzau?

Da yake jawabi kan kujerar Sarkin Zazzau, Bamalli yace kowane ɗa ga sarki yana fatan gadar mahaifinsa, kuma shi bai taɓa tunanin zama sarki ba, sai dai ya yi fatan samun sarauta mai girma.

Alhaji Bamalli yace:

"Fatana shine na zama Magajin Gari ko kuma Madaki, Allah yasan wannan shine fatan da na yi."
"Mun gode wa Allah da ya bamu tsawon rayuwa kuma ya bamu lafiya sannan ya bamu wannan mulki ba don ƙarfin mu ba, ganin damarsa ce ya bamu wannan damar ta gadon iyayenmu."
"Mun gode Allah tare da addu'ar ya taimaka mana wajen sauke nauyin da ya hau kan mu. Ba abinda zamu iya cewa mutanen masarautar Zazzau da jihar Kaduna baki ɗaya sai Godiya."

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Matsalar tsaro a yankin Arewa

Da yake tsokaci kan matsalar tsaro a Arewa, Sarkin ya yi kira ga yan Najeriya su tallafawa gwamnati a yakin da take da matsalar.

"Mun yi taro da gwamnonin Arewa kuma babban maƙasudin taron shine tsaro. Mun tattauna kan abinda ke faruwa a Sokoto ba wai masarautar Zazzau kaɗai ba."
"Matsalar taje kusan ko ina, Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Kaduna Neja, har Nasarawa. Saboda haka matsalar ta shafi kowa."
"Babbar hanyar warware matsalar shine mu koma ga Allah, mu tuba kuma mu cigaɓa da taimakawa kokarin da ake na magance dukkan matsalolin."

A wani labarin na daban kuma Kamfanin sada zumunta Twitter ya yi martani kan kalaman shugaba Buhari na ranar samu yancin kai

Dandalin sada zumunta Twitter ya nuna jin daɗinsa bisa kalaman shugaba Buhari na ɗage hanin da aka masa idan ya cika sharuɗɗa.

A cikin jawabinsa na ranar yancin kai, Buhari yace gwamnati a shirye take ta ɗage hanin amfani da twitter da zaran an cimma matsaya.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel