Matasa zasu iya mamaye manyan kujerun siyasa a babban zaɓen 2023, Saraki

Matasa zasu iya mamaye manyan kujerun siyasa a babban zaɓen 2023, Saraki

  • Tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya yi kira ga matasan Najeriya su tashi daga barcin da suke yi
  • Saraki yace duk wanda ya ɗare kujerar mulki a ƙasar nan to matasa ne suka masa alfarma domin suke da mafi rinjayen kuri'u
  • Yace wajibi kowane shugaba aƙa zaɓa ya tafi da matasa a cikin gwamnatinsa idan ya san cewa suna da ƙarfin canza shi

Abuja - Tsohon shugabana majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya yi kira ga matasa yan Najeriya da su fito a dama da su a babban zaɓen 2023 dake tafe, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Da yake jawabi a wurin taron bikin ranar yanci a Abuja, ranar Jumu'a, Saraki yace wajibi matasa su fito a dama da su saboda babu kyakkyawan jagoranci a ƙasa.

Read also

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

Tsohon gwamnan Kwara ya ƙara da cewa abinda ya kamata yan Najeriya su saka a gaba shine samun shugaban ƙasa, wanda ya cancanta ya jagoranci ƙasar nan.

Bukola Saraki
Matasa zasu iya mamaye manyan kujerun siyasa a babban zaɓen 2023, Saraki Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Wane irin shugaba Najeriya take bukata?

Sanata Saraki yace:

"Ina ganin abinda muka rasa shine samun shugaba nagari, kuma abinda ya fi dacewa mu maida hankali shine samun nagartaccen shugaba."
"Har sai matasa sun tashi tsaye sun fara tambayar kansu, wane gwamna, sanata ko shugaban ƙasa ya dace mu zaɓa, abubuwa ba zasu canza ba."

Matasa ke da yawan kuri'u

Bukola ya ƙara da cewa matasa ke da yawan kuri'u da zasu iya yanke wazai jagorance su, saboda haka wajibi a zuba su a muƙaman gwamnati.

Ya cigaba da cewa:

"Idan kuka zaɓi shugaban da ya dace, kuma yasan cewa kuna da ƙarfin da zaku tsige shi daga ƙujera, to zai tafi da matasa kamar ku a cikin gwamnatinsa."

Read also

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

"Wannan shine dalilin da yasa ya zama wajibi ku wayar da kan matasa yan uwanku, ku nuna wa matasan yanzun cewa kun shirya juya akalar ƙasar nan."
"Idan kuka duba adadin (masu zaɓe), zaku ga cewa kuna musu alfarma ne. Idan rabin matasa 18,000 miliyan da basu da katin zaɓe zasu yi rijista, to kuri'ar matasa ce zata yanke komai."

A wani labarin na daban kuma Gwarazan yan sanda sun ceto iyalan kakakin majalisa da wasu mutum 11 daga hannun miyagu

Jami'an yan sanda a jihar Zamfara, sun samu nasarar kubutar da mutum 5 daga cikin iyalan kakakin majalisar dokokin jihar.

Kwamishinan yan sanda, Ayuba Elkanah, yace jami'ai sun ceto wasu mutum 11 da mahara suka sace a Kauran Namoda.

Source: Legit

Online view pixel