Nasrun minallah: Sojoji sun hallaka yan fashi 394, yan ta'adda 85 a cikin mako uku, DHQ

Nasrun minallah: Sojoji sun hallaka yan fashi 394, yan ta'adda 85 a cikin mako uku, DHQ

  • Hedkwatar tsaro ta bayyana irin nasarorin da rundunar sojin Najeriya ta samu a faɗin kasa cikin makonni uku da suka shuɗe
  • Hedkwatar tace dakarun soji sun hallaka yan fashi 394, da yan ta'adda 85 a hare-hare daban-daban ta sama da ƙasa da suka kaddamar
  • Hakanan ta bayyana cewa dakarun sun kwato makamai da dama, bindigun AK-47, da alburusai

Abuja - Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ), ranar Talata, ta bayyana cewa jami'an sojiji sun sheƙe yan fashi 394, yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a Operation daban-daban cikin mako uku da suka gabata, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Hedkwatar tace an hallaka yan ta'addan ne a ƙauyukan jihar Borno, yayin da yan bindiga suka gamu da ajalinsu a hannun sojoji a jihohin Kaduna, Kano, Zamfara da Taraba.

Kara karanta wannan

Ba ministan tsaro bane da AK-47: Ma'aikatar tsaro ta bayyana wa aka gani da AK-47

Dakarun sojojin Najeriya
Nasrun minallah: Sojoji sun hallaka yan fashi 394, yan ta'adda 85 a cikin mako uku, DHQ Hoto: dw.com
Asali: UGC

Muƙaddashin daraktan watsa labarai na DHQ, Birgediya Janar Bernard Onyeuko, shine ya bayyana haka a wurin taron manema labarai game da ayyukan sojoji daga 2 ga watan Satumba zuwa 30, a hedkwata dake Abuja.

Yan fashi da yan ta'adda nawa aka damƙe?

Yace yan ta'adda da yan fashi kimanin 105, da waɗanda suke haɗa kai da kuma masu garkuwa da mutane ne suka shiga hannu.

Ya ƙara da cewa aƙalla yan ta'addan Boko Haram/ISWSP 2,783 tare da iyalansu sun miƙa wuya ga sojojin cikin wannan ƙankanin lokacin.

Onyeuko ya bayyana cewa sojoji sun kwato makamai kala daban-daban daga hannun yan ta'adda da yan fashi cikin wannan lokacin.

A jawabinsa yace:

"Duka baki ɗaya, an kashe yan ta'addan ISWAP/Boko Haram kuma an kame yan ta'adda da waɗanda suke haɗin guiwa 43 a hare-hare daban-daban. An kuma kwato makamai da suka haɗa da bindigun Ak-47, SMG, HK21, alburusai da sauransu."

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sandan Zamfara suka kama 'yan bindiga 69 da masu haɗa baki da su

"A Zamfara da Kano, sojoji sun hallaka yan bindiga 47, tare da kame yan leƙen asiri, masu tallafa musu da kuma waɗanda suke haɗin guiwa da dama."

Daraktan watsa labarai na DHQ ya bayyana wurare da dama da adadin yan fashi da yan ta'addan da jami'an sojoji suka sheke ciki mako uku, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A wani labarin kuma Shugaban ma'aikata tare da kwamishinoni 4 na gwamnan arewa sun yi murabus daga mukamansu

Shugaban ma'aikata na gwamnatin jihar Benuwai, Orbunde, tare da kwamishinoni 4 sun mika takardar murabus.

Kusoshin gwamnatin gwamna Ortom, sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin samun damar fuskantar siyasar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262