Manyan jiga-jigan APC 3 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas

Manyan jiga-jigan APC 3 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas

  • Yanzu lokaci ne na sauya sheka kuma mambobin jam’iyyun siyasa suna barin jam’iyyarsu ta yanzu saboda bukatunsu
  • Kwanan nan, tsoffin mambobin majalisar wakilai uku suka yanke shawarar barin jam’iyya mai mulki, All Progressives Congress, zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party
  • Gwamna Nyesom Ezenwo Wike, wanda ya yi murna, shine ya tarbi masu sauya shekar zuwa jam'iyyar adawar, yana mai cewa gwamnatin APC ta gaza wa 'yan Najeriya

Fatakwal, jihar Ribas - Tsoffin mambobin majalisar wakilai uku, Hon Ogbonna Nwuke, Hon Iboroma Akpana da Hon Emmanuel Deeyah a ranar Alhamis, 30 ga watan Satumba, sun sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Rivers.

Sauran wadanda suka sauya sheka sun hada da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ribas, Rt Hon Stephen Ezekwem da kuma tsaffin mambobin majalisar guda biyu, Hon Emmanuel Okata da Hon Ibiso Nwuche, Daily Trust ta rahoto.

Read also

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

Manyan jiga-jigan APC 3 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas
Manyan jiga-jigan APC 3 sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Ribas Hoto: Leadership News
Source: Facebook

Da yake tarban wadanda suka sauya sheka a wani biki, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC ta gaza wa ‘yan Najeriya.

Wike ya ce:

"Jam'iyyar APC ta gaza wa Najeriya. Ina ci gaba da fada musu; su bari APC a Jihar Ribas ta gaya mana abin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa mutanen Jihar Ribas a cikin shekaru shida da suka gabata.”

Ya bayyana fatan cewa PDP za ta kayar da APC a babban zaben 2023 sannan ya ba da tabbacin cewa PDP ba za ta taba rabuwa ba saboda jam'iyyar ita ce fatan 'yan Najeriya a zabe mai zuwa, jaridar The Punch ta ruwaito.

Wike ya bukaci magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar da kada su yarda wani ya razana su.

Read also

Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu

A halin da ake ciki, jam'iyyar APC reshen jihar Ribas ta bayyana sauya shekar mambobinta zuwa PDP a matsayin dirama.

Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

A wani labarin, gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anambra daga wasu jam'iyyu zuwa APC.

Ana ci gaba da yawaita sauya sheka a cikin wannan shekara, lamarin da ya kawo cece-kuce a jam'iyyun siyasa daban-daban na Najeriya.

Legit.ng Hausa ta lura cewa, akalla 'yan majalisa daga jihar Anambra 11 suka sauya sheka zuwa APC wanda gwamnan ya karbe su cikin lumana.

Source: Legit

Online view pixel