Yan kwaya da masu fataucin bindiga suka lalata Fulani Makiyaya, Sheikh Ahmad Gumi

Yan kwaya da masu fataucin bindiga suka lalata Fulani Makiyaya, Sheikh Ahmad Gumi

  • Sheikh Ahmad ya bayyana hanyar kawo karshen laifukan da Fulani ke aikatawa cikin daji
  • Babban Malamin ya yi jawabi a taron da aka shirya a Arewa House dake Kaduna
  • A cewar Gumi, Fulani shima dan Adam ne kuma dole ne a mutuntashi

Kaduna - Shahrarren Malaman addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa dillalan muggan kwayoyi da masu fataucin makamai ne suka mayar da Fulani Makiyaya yan bindiga.

Fulani Makiyaya a shekarun nan sun addabi al'ummar Najeriya, musamman yankin Arewa maso yamma.

Sheikh Gumi ya kasance mutum daya tilo da samu ganawa da yan bindiga domin yi musu wa'azi su daina garkuwa da mutane.

Malamin a jawabin da yayi a taron zaman lafiya da cibiyar mutunta rayukan mutum ta shirya a Arewa House dake jihar Kaduna ranar Alhamis, rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Gumi ya ce hanya daya tilo da za'a bi domin kawo karshen barandanci shine raba alakar dake tsakanin dillalan kwayoyi da makamai da kuma Makiyaya.

Yace:

"Idan mugayen mutane sun ja hankalinsu, yan kwaya, masu fataucin bindiga, kada mu bari a yi amfani da su.
Wajibi ne mu dawo da su cikin al'umma, abinda muke bukata kenan. Su ma ya kamata a mutuntasu, kuma a basu dukkan hakkokinsu na dan Adam."

Yan kwaya da masu fataucin bindiga suka lalata Fulani Makiyaya, Sheikh Ahmad Gumi
Yan kwaya da masu fataucin bindiga suka lalata Fulani Makiyaya, Sheikh Ahmad Gumi Hoto: Dr Ahmad Gumi
Asali: Facebook

Sheikh Gumi ga 'yan Arewa: Hanyoyin da za ku zauna lafiya da 'yan bindiga

Ahmad Gumi, ya shawarci mutanen yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da ta’addanci kan yadda za su zauna lafiya tare da ‘yan bindigar da ke mamaye dazuzzukan su.

Malam Gumi ya ce mutane za su iya habaka "alakar juna da 'yan bindiga ba tare da an cutar da su ba",

Kara karanta wannan

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

An nakalto malamin yana fadi yayin da yake gabatar da lacca a jami'ar ABU da ke Zariya a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel