Pantami na neman ganin an sauƙaƙa wa 'yan Nigeria kuɗin data

Pantami na neman ganin an sauƙaƙa wa 'yan Nigeria kuɗin data

  • Isa Ali Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya ce gwamnati na aiki don ganin an samu saukin kudin data
  • Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja yayin wani taro na intanet da aka yi
  • Ministan ya ce gwamnati na aiki tare da masu ruwa da tsaki a bangaren don ganin an rage kudin ta yadda talakawa za su iya siya

FCT, Abuja - Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, a ranar Alhamis, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na ganin ta saukaka farashin kudin data don shiga intanet, The Punch ta ruwaito.

Pantami, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taro da aka yi na Intanet a Abuja ya kara da cewa gwamnatin tana aiki don ganin farashin data/intanet ya yi sauki ta yadda talaka sai iya siya.

Read also

Telegram ta yi fintinkau yayin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki

Pantami na neman ganin a sauƙaƙa wa 'yan Nigeria kuɗin data
Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami. Hoto: The Punch
Source: Facebook

Ministan ya ce ana aiki don magance abubuwan da ke saka kudin data tsada da suka hada da tsaro da fasahar sadarwar da sauransu.

Pantami ya ce:

"Akwai abubuwa da dama da za a yi a bangaren samar da intanet a yankunan karkara, kashi 10 cikin 100 ne kawai suke da ingantaccen kayayyakin intanet.
"Don haka, muna aiki don ganin an samar da intanet din ga kauyuka. Don haka ne muke yin tsare-tsare don magance kallubalen da suka saka data ke tsada.
"Kudin madaidaicin data ya kai 1200 a 2019 amma a yanzu ya sauka da kashi 50 cikin 100, kimanin 500.
"A waje na, ban gamsu da wannan ba. Ya zama dole mu cigaba da aiki don tabbatar da cewa farashin data ya yi sauki ta yadda talakawa za su iya siya.

Read also

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

"Bugu da kari, muna aiki don magance abubuwan da ke kara tsadar samar da datan. Kafin yanzu a kan caji 6000 domin izinin amfani da kasa (RoW) amma ya yanzu ya koma kimanin 145.
"Daya daga cikin abin da ke saka data tsada kuma shine tsaro. Shugaban kasa ya umurci ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro ya bawa dukkan kamfanonin sadarwa kariya kyauta. Hakan ya saukaka kudin samar da datan.
"Kazalika, muna aiki tare da ma'aikatan kudi, kungiyar gwamnoni da majalisar kolin tarayya don magance matsalar karbar haraji fiye da daya kuma muna samun nasarori."

Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Fasahar 5G, Masani Daga Kano Ya Yi Fashin Baƙi

A wani labarin daban, Mallam Shehu Auwal masanin fasahar sadarwar zamani da kwamfuta, mazaunin Kano a Nigeria ya yi fashi baki kan fasahar 5G.

A cikin ƴan kwanakin nan ne ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami sanar da cewa za a fara aiki da fasahar 5G a kasar a watan Janairun 2022.

Read also

Hoton tsohon rasit da ke nuna an siya buhu 40 na siminti kan N1520 ya janyo cece-kuce

A kan wannan gabar ne Legit.ng Hausa ta tuntunbi masanin fasahar sadarwa zamani da kwamfuta, Mallam Shehu Auwal mazaunin Kano ya fede biri har wutsiya game da batun.

Source: Legit.ng

Online view pixel