Gumi: Jini mai yawa ne ke kwaranya a Najeriya, an kasa tsayar da shi
- Sanannen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya koka da yadda jini ke kwaranya a kasar nan
- Gumi ya ce a shekaru 3 da suka gabata Najeriya ta kashe dala 1b wurin yaki da rashin tsaro, wanda kashi goma ya isa a wayar da kan miyagun
- Malamin ya ce rashin addini, jahilci da rashin wayewar kai ce ke damun 'yan ta'addan, amma wayar musu da kai zai kawo karshen matsalar
Kaduna - Fitaccen malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce jini mai matukar yawa ne ke kwaranya a Najeriya, Daily Trust ta wallafa.
A yayin jawabi a wani taron tabbatar da zaman lafiya wanda Center For the Advancement of Human Dignity and Value (CAHDV) tta shirya a Kaduna a ranar Alhamis, malamin ya ce ya na mamakin yadda ba a dauka mataki ba kan zubar jinin ba.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce rashin addini, ilimi da kuma wayewar kai a fannin 'yan ta'adda shi ne abinda ke kawo hauhawar rashin tsaro a yankin kuma maganin shi shine wayar da kai.
Kamar yadda Gumi ya ce, a shekaru uku da suka gabata, kasar nan ta kashe dala biliyan daya wurin yaki da 'yan bindiga kuma ya ce ana bukatar wata dala biliyan dayan domin cigaba da yakar hakan, kashi goma kenan daga cikin abinda ake bukata wurin wayar da kan 'yan bindigan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na gane wani abu daya, rashin addini, rashin ilimi, da jahilci ne abinda ya kawo rashin tsaro kuma maganinsa shi ne a wayar da kai. Idan aka wayar da su, za a iya magance matsalar. Idan ana son shawo kan matsalar kamar yadda aka kirkire ta, sai an je cikin jinin kuma hakan mu ke fuskanta a halin yanzu.
"Abinda mu ke fuskanta a yau shi ake kira da rashin wayewa. Ga jini nan ya na ta kwaranya babu dalili kuma har yanzu ba mu gane darajar dan Adam ba balle amfaninsa. Dan Adam ya na daraja ba kadan ba, ba a iya tilasta addini a kan kowa. Me yasa jini ke kwaranya a kasar nan?"
EFCC ta dire gefe, ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin Orji Kalu
A wani labari na nan, hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, za ta daukaka kara kan hukuncin da Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotu tarayya ya yanke ta hana ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Kalu a halin yanzu sanata ne wanda aka taba yanke wa hukuncin shekaru 12 a gidan maza kan handamar N7.1 biliyan amma kotun koli ta soke hukuncin a ranar 8 ga watan Mayu.
Sai dai, kotun kolin ta bukaci a sake gurfanar da Kalu a babbar kotun tarayya. Kalu ya amfana daga wannan hukuncin inda aka sako shi daga gidan yarin Kuje, ya kuma sake mika bukata gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja da ta hana sake gurfanar da shi.
Asali: Legit.ng