EFCC ta dire gefe, ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin Orji Kalu

EFCC ta dire gefe, ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin Orji Kalu

  • EFCC ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin da kotun tarayya ta yanke tsakaninta da Sanata Orji Kalu
  • Hukumar ta ce babu shakka akwai kuskure a hukuncin, ganin cewa soke shari'ar da kotun koli ta yi ba wanke shi ta yi daga laifi ba
  • An yanke wa Sanata Kalu hukuncin zaman shekaru 12 a gidan maza sakamakon kama shi da aka yi da laifin handamar biliyan 7.1

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, za ta daukaka kara kan hukuncin da Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotu tarayya ya yanke ta hana ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu.

Kara karanta wannan

Jami'an NSCDC sun cafke abokin harkallar 'yan bindiga dauke da karamar bindiga

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Kalu a halin yanzu sanata ne wanda aka taba yanke wa hukuncin shekaru 12 a gidan maza kan handamar N7.1 biliyan amma kotun koli ta soke hukuncin a ranar 8 ga watan Mayu.

EFCC ta dire gefe, ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin Orji Kalu
EFCC ta dire gefe, ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin Orji Kalu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Sai dai, kotun kolin ta bukaci a sake gurfanar da Kalu a babbar kotun tarayya. Kalu ya amfana daga wannan hukuncin inda aka sako shi daga gidan yarin Kuje, ya kuma sake mika bukata gaban wata babbar kotun tarayya a Abuja da ta hana sake gurfanar da shi.

A hukuncin da Mai shari'a Ekwo ya yanke a ranar 29 ga watan Satumban 2021, an amince da bukatar tsohon gwamnan kan cewa kotun koli ba ta ce a sake gurfanar da shi ba dogaro da wani sashi na gyararren kundun tsarin mulki da ya ce "ba za a iya sake gurfanar da mutum kan laifi ba bayan an wanke shi daga laifin".

Kara karanta wannan

An cafke wani sojan karya da abokinsa da ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

EFCC ta sakankance cewa alkalin ya yi kuskure kan shari'ar saboda sashi na 36, sakin layi na 9 na kundun tsarin mulkin 1999 zai yi tasiri ne idan hukuncin farkon kotu ce ta yi.

A saboda haka, kotun kolin ta kwatanta wanke Kalu da ta yi da soke shari'ar saboda alkalin kotun daukaka kara ne a yanke hukuncin.

Hukumar ta kara da cewa kotun ta yi kuskure inda ta ce kotun koli ba ta bada umarnin sake gurfanar da Kalu ba.

Farmaki: Mazauna wasu garuruwa a Kaduna sun bar gidajensu, suna neman daukin gwamnati

A wani labari na daban, a ranar Talata, jami'an tsaro sun kara samo gawawwaki uku a kauyukan Madamai da Kacecere da ke kananan hukumomin Kaura da Zangon Kataf, lamarin da yasa yawan mamatan ya kai har arba'in da biyar.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

Daily Trust ta tattaro cewa, za a yi birniyar wasu daga cikin mamatan a kauyen Madamai da ke karamar hukumar Kaura a ranar Alhamis yayin da aka birne wasu kamar yadda addinin Islama ya tanada a ranar Litinin a karamar hukumar Zangon Kataf.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan a ranar Talata ya ce rahotannin tsaro sun bayyana cewa an sake samun karin gawawwaki 3, biyu daga harin Madamai, daya kuma a harin Kacecere.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel