Shugaban ma'aikata da kwamishinoni 4 na gwamnan Jam'iyyar PDP sun yi murabus

Shugaban ma'aikata da kwamishinoni 4 na gwamnan Jam'iyyar PDP sun yi murabus

  • Shugaban ma'aikata na gwamnatin jihar Benuwai, Orbunde, tare da kwamishinoni 4 sun mika takardar murabus
  • Kusoshin gwamnatin gwamna Ortom, sun bayyana cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin samun damar fuskantar siyasar 2023.
  • Wannan matakin nasu ya zo ne bayan umarnin gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, cewa duk mai son fara siyasar 2023 ya aje muƙaminsa

Benue - Shugaban ma'aikata na gwamnan Benuwai, Fasto Terwase Orbunde, tare da wasu kwamishinoni huɗu sun miƙa takardar murabus domin samun damar fuskantar siyasar 2023.

Kwamishinonin hudu sun haɗa da, kwamishinan yaɗa labarai, Mrs Ngunan Addingi, da kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa, Dondo Ahire.

Sauran sune kwamishinan ilimi, Farfesa Dennis Ityayvar, da kuma kwamishinan matasa da wasanni, kwamaret Ojemba Ojotu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Gwamna Samuel Ortom
Shugaban ma'aikata da kwamishinoni 4 na gwamnan Jam'iyyar PDP sun yi murabus Hoto: channesltv.com
Asali: UGC

Wane muƙami suke nema a 2023?

Tsohon shugaban ma'aikata, Orbunde, tsohon kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa da kuma tsohon kwamishinan Ilimi, kowannen su na fatan ya gaji gwamnan jihar, Samuel Ortom.

Kara karanta wannan

Jagororin PDP sun fara yaki domin David Mark ko Makarfi ya karbi shugabancin Jam’iyya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da tsohuwar kwamishinan yaɗa labarai, Addingi, da takwaranta tsohon kwamishinan matasa da wasanni, Ojutu, na shirye-shiryen taka takarar yan majlisar wajilai a mazaɓunsu.

Tsaffin makusantan gwamnan Benuwai, sun tabbatar da murabus ɗin su ga manema labarai a Makurɗi, babban birnin jihar.

Na gama aikina, zan tunkari gaba - Orbunde

A wani jawabi da tsohon shugaban ma'aikata, Orbunde, ya fitar, ya bayyana cewa ya kammala aikin da ya kudiri yi, yanzun kuma zai fuskanci aiki na gaba a matsayin gwamna Idan Allah ya so.

Yace:

"Mun fara wannan tafiyar ne tun a shekarar 1995, lokacin da gwamnan Ortom ya nemi na zo mu yi gwagwarmayar yaƙin neman zaɓen Gwamna."
"Kuma tun wancan lokaci muke aiki tuƙuru har mafarkinmu ya zama gaskiya a shekarar 2015."
"Duk da an samu matsaloli a tafiyar amma Allah ta hanyar mutanen jihar Benuwai ya baiwa uban gidan na nasara a 2015 da kuma 2019. Kuma na kasance cikin gwamnati na tsawon zangon biyu."

Kara karanta wannan

Ta fashe: Sirrin kazamar dukiyar shugabannin duniya 35, 'yan siyasa 330 da biloniyoyi 130 a kasashe 91

A wani labarin na daban gwamnatin jihar Zamfara ta damƙe yan leken asirin yan bindiga sama da 2,000 tun bayan datse sadarwa

Kwamishinan yaɗa labarai da Al'adu na jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Dosara, yace ɗauke sabis a Zamfara ya haifar da ɗa mai ido.

Dosara yace zuwa yanzun hukumomin tsaro sun samu nasarar damke yan leken asirin yan bindiga sama da 2,000 cikin kwana 30.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262