Wike ya caccaki gwamnonin da suka dogara da kudaden shiga daga tarayya, ya ce babu wata jaha da ke a talauce

Wike ya caccaki gwamnonin da suka dogara da kudaden shiga daga tarayya, ya ce babu wata jaha da ke a talauce

  • Gwamna Nyesom Wike ya kira takwarorin sa da suka dogara kacokan kan kudaden da gwamnatin tarayya ke ware masu
  • Wike ya shawarci gwamnonin da kada su dogara da irin wadannan kudade, yana mai lura da cewa babu wata jiha a kasar nan da ke fama da talauci ko rashin albarkatun da za su rayu
  • Ya kara da cewa duk da akwai kalubale, ya kamata gwamnoni su iya sarrafa abubuwan da suke akwai a jihohin su

Fatakwal, jihar Ribas - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya caccaki gwamnoni da ke dogaro da kason kudin da gwamnatin tarayya ke aike masu, yana mai cewa babu wata jiha a Najeriya da ke a talauce.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ya bayyana wannan matsayin ne yayin da yake gabatar da jawabi taron Cibiyar Nazarin Tsaro ta Kasa a Abuja a ranar Laraba, 29 ga watan Satumba.

Read also

Duk da tsoma bakin Diflomasiyya: 'Yan Ghana sun cigaba da muzguna wa 'yan kasuwan Najeriya

Wike ya caccaki gwamnonin da suka dogara da kudaden shiga daga tarayya, ya ce babu wata jaha da ke a talauce
Wike ya caccaki gwamnonin da suka dogara da kudaden shiga daga tarayya, ya ce babu wata jaha da ke a talauce Hoto: Rivers State Government House
Source: Facebook

Wike wanda ya caccaki takwarorinsa dake dogaro da kudaden shiga na wata-wata daga Asusun Tarayya (FAAC) ya bukace su da su yi amfani da albarkatun da ke cikin jihohin su yadda ya kamata.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Babu jihar da ke fama da talauci a kasar nan. Irin wannan dogaro da Gwamnatin Tarayya ne ya sanya wasu talaucewa. A karshen kowane wata, suna aika Babban Akanta-Janar/Kwamishinan Kudi hukumar FAAC.”

Wike ya yi mamakin dalilin da yasa gwamnoni ke kukan babu kudi a jihohinsu amma suke neman wa'adin mulki na biyu, Channels TV ta kuma ruwaitowa.

Ya yanke hukunci kamar haka:

“Duk jihar da ta ce talaka ce ita tana yaudarar ku ta hanyar faɗin haka. Ina ci gaba da fada musu, idan jihar ka talaka ce, me ya sa kake son zama gwamna? Jihar ka talaka ce; kake son tsayawa takara a karo na biyu.”

Read also

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

Gwamnan ya lura cewa kowace jiha tana da nata fa'ida da rashinsa, amma ya yi imanin ci gaba na iya faruwa idan gwamnoni za su iya amfani da damar don amfanin jihar su da jama'ar ta.

Jerin sunaye: BudgIT ya bayyana jihohin Najeriya 5 mafi kokari a 2021

A baya mun kawo cewa, BudgIT, wani kamfani na fasaha da ke bayani dalla-dalla kan lamuran da suka shafi kudi, a ranar Laraba, 29 ga Satumba, ya fitar da rahotonsa na shekara wanda ke bayyana jihohi mafi kokari kuma mafi gazawa a Najeriya.

A cikin rahoton, kamfanin ya bayyana cewa jihohi biyar sun fito a matsayin waɗanda suka haɓaka kokarinsu ta bangaren kuɗi da matakan dorewa.

Kamfanin ya yi bayanin cewa rahotonsa ya yi la’akari ne da kudaden shiga na jihohi (IGR) wanda Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta wallafa.

Source: Legit.ng

Online view pixel