Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon Ministan Abuja, Yan sanda sun kaddamar da binciken ceto shi

Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon Ministan Abuja, Yan sanda sun kaddamar da binciken ceto shi

  • Miyagun yan fashin daji sun yi awon gaba da tsohon ministan Abuja, Solomon Ewuga, a kan hanyarsa ta zuwa Abuja
  • Bayan samun wannan rahoton, jami'an yan sanda sun yi gaggawar kai ɗauki cikin daji, kuma sun samu nasarar ceto shi
  • A halin yanzun kakakin yan sandan Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da cewa jami'an yan sandan sun bazama neman miyagun

Nasarawa - Tsohon ƙaramin ministan Abuja, Solomon Ewuga, ya shiga hannun miyagun yan bindiga, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan sun sace Ewuga da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a Kurmin Shinkafa, kusa da garin Gudi a ƙaramar hukumar Akwanga, jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon Ministan Abuja a jihar Nasarawa
Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon Ministan Abuja, Yan sanda sun kaddamar da bincike ceto shi Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ranar Laraba.

Yace tuni hukumar yan sanda ta tada tawagar jami'an yan sanda domin ceto tsohon ministan kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa.

Nansel ya bayyana cewa duk da har yanzun ba'a damƙe ko mutum ɗaya ba, amma hukumar zata tabbatar da duk me hannu a lamarin ya fuskanci hukunci.

This Day ta ruwaito Nansel yace:

"Tsohon sanatan yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja lokacin da maharan suka yi awon gaba da shi, amma saboda ɗaukar matakin gaggawa da jami'an yan sanda suka yi bayan samun rahoto, sun shiga daji kuma sun ceto shi."
"Babu wanda aka cafke yanzu, amma hukumar yan sanda bata haƙura ba, kuma sai mun tabbatar da an hukunta waɗanda suka aikata haka."

Kara karanta wannan

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

"A yanzun da nake magana da ku, kwamishinan yan sanda, Adesina Soyemi, ya umarci jami'ai su shiga cikin dajin domin kamo maharan."

A wani labarin kuma Baku isa ku tilasta mana mu baku shugabancin Najeriya ba, El-Rufa'i ya fadawa Gwamnonin Kudu

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya faɗawa gwamnonin kudu cewa ba zasu tilastawa arewa ta mika musu mulki ba.

A cewar gwamnan, kundin tsarin mulki bai tanaji mulkin karɓa- karɓa ba, kuma jam'iyyar APC bata amince da haka ba a dokokinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262