Baku isa ku tilasta mana mu baku shugabancin Najeriya ba, El-Rufa'i ya fadawa Gwamnonin Kudu

Baku isa ku tilasta mana mu baku shugabancin Najeriya ba, El-Rufa'i ya fadawa Gwamnonin Kudu

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya faɗawa gwamnonin kudu cewa ba zasu tilastawa arewa ta mika musu mulki ba
  • A cewar gwamnan, kundin tsarin mulki bai tanaji mulkin karɓa-karɓa ba, kuma jam'iyyar APC bata amince da haka ba a dokokinta
  • Yace a PDP ne akwai wannan dokar amma su yan kudu da kansu suka karya ta lokacin mulkin marigayi Yar'adua

Kaduna - Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, yace gwamnonin kudu ba zasu tilastawa Arewa ta miƙa shugabancin Najeriya ga yankinsu ba, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

El-Rufa'i ya faɗi haka ne yayin da yake tsokaci kan bukatar gwamnonin kudu cewa yankinsu ne zai fitar da shugaban ƙasa da zai gaji Buhari.

Malam Nasiru, wanda ya bada shawarar baiwa kudanci shugaban ƙasa, yace gwamnonin kudu sun ɗauki abun da zafi, da har zasu ce wajibi a ba su shugaban ƙasa a 2023.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

Malam Nasiru El-Rufai
Baku isa ku tilastana mana mu baku shugabancin Najeriya ba, El-Rufa'i ya fadawa Gwamnonin Kudu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Malam Nasiru yace:

"Ba zaku tilasta mana sai mun baku shugaban ƙasa ba, amfani da kalmar 'Ɗole' na nufin ko muna so ko bamu so, meyasa zaku kawo batun wajibi a harkokin siyasa?"
"Babu wani abu mulkin karba-karba a kundin tsarin mulki, waɗannan abubuwan ana yinsu ne domin haɗin kai da sulhu."
"Kowace jam'iyyar siyasa tana da nata dokoki kuma babu wata doka a APC da muka amince za'a yi mulkin karba-karba."

Ko akwai mulkin karba-karba a jam'iyyar PDP?

Bugu da ƙari gwamna El-Rufa'i yace jam'iyyar PDP da ke da tsarin mulkin kama-kama, "Sun karya dokar lokacin mulkin marigayi shugaba Umaru Musa Yar'adua da Goodluck Jonathan."

"Saboda haka, wani ya fito yace kada ɗan Najeriya ya nemi shugaban ƙasa kawai saboda yankin da ya fito, babu makamancin haka a kundin tsarin mulki."

Kara karanta wannan

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Gwamnan yace takwarorin nasa sun yi azarɓaɓin fitowa kafar watsa labarai su ayyana kudirinsu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A cewarsa kamata ya yi su nemi yan uwansu na yankin arewa, a zauna taro, domin cimma matsaya kan lamarin.

A wani labarin kuma Manoma Sama da 20 Sun Mutu, Yayin da Jirgin Yaki Ya Yi Kuskuren Sakin Bama-Bamai a Borno

Wani sabon harin bama-bamai ta sama ya yi sanadiyyar hallaka mutanen da basu ji ba basu gani aƙalla 20 a Borno.

Harin, wanda aka kai ƙauyen Dabar Masara dake ƙaramar hukumar Monguno, ranar Lahadi, ya shammaci mutanen ƙauyen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel