El-Rufai: Sakarci ne ka kalmashe a Legas ko Fatakwal kana son a miko muku mulki

El-Rufai: Sakarci ne ka kalmashe a Legas ko Fatakwal kana son a miko muku mulki

  • Gwamnan jihar Kaduna, ya ce babban sakarci ne a ce mutum ya kalmashe kafa a Legas ko Fatakwal kuma ya ce ga wanda 'yan arewa za su zaba
  • Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sake jaddada cewa, in har kudu na son mulki, kamata yayi su roka arewa ba su ce dole sai an mika musu ba
  • Gogaggen dan siyasan ya ce babu tsarin mulkin karba-karba a kundun tsarin mulkin kasar nan, don haka takwarorinsa na kudu su ja da baya

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi karin haske kan matsayar kungiyar gwamnonin arewa kan mika mulki kudancin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito hakan.

A wani taro a Kaduna a ranar Litinin, gwamnonin sun ce mulkin karba-karba na shugabancin kasa ba ya daga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

El-Rufai: Sakarci ne ka kalmashe a Legas ko Fatakwal kana son a miko muku mulki
El-Rufai: Sakarci ne ka kalmashe a Legas ko Fatakwal kana son a miko muku mulki. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

Sun sanar da hakan ne yayin martani ga bukatar takwarorinsu na kudu wanda suka bukaci yankinsu ya samar da shugaban kasa a nan gaba.

A zantawar da yayi da manema labarai, El-Rufai ya ce kada wanda yayi tsammanin cewa zai iya kalmashe kafafu a Legas ko Fatakwal kuma ya yanke hukuncin abinda ya dace arewa ta yi ko wa ya dace 'yan arewa su zaba.

Ya ce in har kudu na son mulki, toh ta shirya tattaunawa da arewa tare da sasanci har a fitar da wanda ya dace a zaba, ba wai a nemi saka wa arewa yin abu dole ba.

"Ba mu ce ba za a iya mulkin karba-karba ba, za a iya amma dole ne ku zo ku zauna da 'yan siyasar arewa kuma ku tattauna kafin su amince tare da baku goyon baya.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

"Amma babu wanda ya isa ya zauna Legas ko Fatakwal kuma ya ce ga abinda 'yan arewa za su yi, ko kuma dole a mika mulki kudu, wannan ba daidai bane kuma ba yadda ake siyasa bane. Tsabar sakarci ne."

Daily Trust ta ruwaito cewa El-Rufai na daga cikin gwamnonin farko da ya fara rokon a bai wa kudancin kasar nan mulki.

A shekarar da ta gabata, ya ce adalci da hadin kai na arewa ne zai bayyana idan aka mika mulki kudancin kasar nan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika wa'adin mulkinsa.

Bayan El-Rufai, gwamnoni kamar Babagana Umara Zulum na jihar Borno, Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Aminu Bello Masari na jihar Katsina sun bi bayansa.

Rahoto: Yadda datse layikan sadarwa ke barazana ga kasuwanci a arewa maso yamma

A wani labari na daban, kasuwanci ne a halin yanzu ke jin tsanani kan hukuncin gwamnati na datse layikan sadarwa a wasu jihohin arewa maso yamma na kasar nan kamar yadda rahotannin SB Morgan suka bayyana, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Osinbajo ya bayyana halin da yankunan kasar nan za su shiga idan Najeriya ta rabu

Rahotan mai taken; "Hostile reception - The impact of telephony shutdowns in North-West Nigeria," wanda aka bincike mutum 679 a makon tsakiyan watan Satumban 2021 domin duba abinda datse kafofin sadarwa suka janyo.

A ranar 3 ga watan Satumba, an bukaci hukumar sadarwa da ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin datse sabis a Zamfara domin shawo kan miyagun al'amuran 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel