Gwamnatin Buhari ta amince maza su ke tafiya hutu idan matansu sun haihu

Gwamnatin Buhari ta amince maza su ke tafiya hutu idan matansu sun haihu

  • Gwamnatin tarayya ta amince da ba maza hutun kwanaki 14 yayin da matansu suka samu karuwa
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake zaman majalisar zartarwa na mako-mako da ya gudana a Abuja a yau Laraba
  • A baya, hukumar NITDA ta samu nasarar ba da irin wannan izini ga ma'aikatar hukumar a watan Maris

Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da hakkin hutun kwanaki 14 na haihuwa ga ma’aikatan gwamnatin tarayya maza domin ba su damar sabawa da jariran da aka haifa musu.

Shugaban ma’aikatan tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnati a ranar Laraba, bayan taron FEC na makon nan wanda Yemi Osinbajo (SAN) ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, The Nation ta ruwaito.

Read also

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Yanzu: Gwamnatin Buhari ta amince maza su ke tafiya hutu idan matansu sun haihu
An amince da kwanaki 14 ga maza idan matansu sun haihu | Hoto: thenationonlineng.net
Source: UGC

Ta ce an yi haka ne don ba da damar habaka kauna da kusanci tsakanin uba da jariri, ko haifaffe ko dan riko, musamman a farkon kwanakin rayuwar yaron.

Misis Yemi-Esan ta ci gaba da bayanin cewa ubannin jariran da aka dauka a matsayin 'yan riko da ba su wuce watanni hudu ba suma za su mori wannan karimcin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda lamarin ya faro

Wannan ci gaban na zuwa ne watanni bayan gwamnatin tarayya ta amince da hutun haihuwa ga ma’aikatan hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA).

Da yake jawabi a yayin bikin kaddamarwa da gabatar da yanayin ayyukan ma’aikatan NITDA, wanda aka gudanar a Abuja, ministan sadarwa da tattalin arzikin dijital, ya ce ci gaban ya yi daidai da sabon tsarin aiki na ma’aikata a hukumar.

Kafin amincewa ga ma’aikatan NITDA a cikin Maris 2021, babu wani tanadi na hutun haihuwa ga ma’aikatan gwamnati, yayin da ma’aikata mata ke da damar hutun haihuwa na watanni uku.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Majalisar wakilai, a shekarar 2018, ta yi watsi da kudirin neman ba da hutun haihuwa ga maza masu aure.

A halin yanzu, wasu jihohi a kasar - ciki har da Legas da Enugu - sun amince da hutun haihuwa ga ma'aikata, inji rahoton The Cable.

Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja

A wani labarin, Majalisar dattijai a ranar Talata ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da Naira biliyan 300 a matsayin kudin taimakon gaggawa don gyara munanan hanyoyi a jihar Neja.

Wannan kuduri na babban zauren ya biyo bayan wani kudiri kan lalacewar hanyoyi a fadin jihar Neja da toshe hanyoyin ta hanyar nuna rashin amincewa da direbobin tirela da direbobin tanka suke yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Mataimakin Babban Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abudullahi, mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudirin, in ji rahoton The Nation.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Source: Legit.ng

Online view pixel