Jerin abubuwa 3 masu ratsa zuciya da mijin tsohuwar minista yayi kafin a harbe shi

Jerin abubuwa 3 masu ratsa zuciya da mijin tsohuwar minista yayi kafin a harbe shi

Labari mai raɗaɗi na kisan Dakta Chike Akunyili, mijin marigayiya tsohuwar ministar watsa labarai, Farfesa Dora Akunyili, ya kasance tamkar fama miki ga 'yan Najeriya tsakanin Talata, 28 ga Satumba da Laraba, 29 ga Satumba.

Wani amininsa da ya zanta da jaridar The Nation ya bayyana cewa marigayi Akunyili ya kasance tare da membobin kungiyar tsoffin daliban jami’ar Najeriya Nsukka (UNAA) a Sharon Hall, All Saints Cathedral, Onitsha, a ranar Talata sa’o’i kafin a kashe shi.

Jerin abubuwa 3 masu ratsa zuciya da mijin tsohuwar minista yayi kafin a harbe shi
Jerin abubuwa 3 masu ratsa zuciya da mijin tsohuwar minista yayi kafin a harbe shi Hoto: Vanguard
Source: Facebook

Majiyar ta lissafa kusan abubuwa uku da marigayin ya aikata kafin kisan nasa.

1. Ya yi magana mai dadi game da marigayiyar matarsa

Mai maganar ya bayyana cewa yayin da yake ba da jawabinsa a taron, Akunyili ya yi magana cikin annashuwa game da ƙaunatacciyar matarsa ​​wacce mutuwa ta raba shi da ita a watan Yunin 2014.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

2. Marigayi Akunyili ya ba da gudummawa ga ƙungiyar

A cewar abokin nasa wanda ba a bayyana sunansa ba, Akunyili, kasancewar shi mutumin kirki, ya ba da gudummawar N500, 000 ga ƙungiyar yayin taron.

3. Rungume dansa kafin su rabu

Bayan taron, majiyar ta ce ta kalli mijin tsohuwar shugabar ta NAFDAC yana rungume da daya daga cikin 'ya'yansa, Obum, kafin daga bisani suka raba hanya.

Majiyar ta kara da cewa a halin yanzu Obum yana aiki tare da gwamnatin jihar Anambra.

'Yan bindiga sun kashe mijin marigayiya Dora Akunyili

A baya mun kawo cewa, wani rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa ‘yan bindiga sun kashe Dr. Chike Akunyili, mijin tsohuwar Ministar Yada Labarai, Farfesa Dora Akunyili.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kashe shi a Umuoji da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra da yammacin ranar Talata, 28 ga watan Satumba.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Kodayake har yanzu babu cikakken bayanai game da lamarin, wata majiya ta kusa da iyalan ta ce marigayin yana nan a taron kungiyar tsoffin daliban Jami’ar Najeriya Nsukka (UNAA) inda aka karrama marigayiya Dora wasu sa’o’i kafin a kashe shi.

Source: Legit

Online view pixel