An Kuma, Manoma Sama da 20 Sun Mutu, Yayin da Jirgin Yaki Ya Yi Kuskuren Sakin Bama-Bamai a Borno

An Kuma, Manoma Sama da 20 Sun Mutu, Yayin da Jirgin Yaki Ya Yi Kuskuren Sakin Bama-Bamai a Borno

  • Wani sabon harin bama-bamai ta sama ya yi sanadiyyar hallaka mutanen da basu ji ba basu gani aƙalla 20 a Borno
  • Harin, wanda aka kai ƙauyen Dabar Masara dake ƙaramar hukumar Monguno, ranar Lahadi, ya shammaci mutanen ƙauyen
  • Har zuwa yanzun rundunar sojojin sama ba ta ce komai ba game da kuskuren kai hari kan mutanen da ba ruwansu

Borno - Aƙalla mutanen ba basu ji ba basu gani ba 20 sun rasa rayukansu sanadiyyar harin jirgin yaƙi a Dabar Masara, ƙaramar hukumar Monguno, jihar Borno, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A cewar wata majiya daga yankin, harin saman ya faru ne ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba da yammaci.

Lamarin ya faru ne dai-dai lokacin da mafi yawancin yan ƙauyen sun tafi gona, wasu kuma sun fita wurin sana'ar kamun kifi.

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

Harin jirgin sama
An Kuma, Manoma Sama da 20 Sun Mutu, Yayin da Jirgin Yaki Ya Yi Kuskuren Sakin Bama-Bamai a Borno Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya harin ya faru?

Wani mazaunin yankin, Ahmadu Tijjani, ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mafi yawan mutane sun fita zuwa gonakinsu lokacin da jirgin ya keta ta yankin baki ɗaya kuma ya saki bama-bamai a wurare uku mabanbanta, dukka a yankin Dabar Masara."
"A ɗaya daga cikin wurin da ya saki bam ɗin, mun samu labarin an gano gawar mutum 10, har an yi musu jana'iza."
"Ina tsammanin sun yi kuskure ne, yan Boko Haram suka hara, amma waɗannan yan uwanmu ne. Sun fita neman abinci ne, domin idan sun zauna babu mai basu abinda za su ci."

Ina ne Dabar Masara?

Ƙauyen Dabar Masara, wuri ne da ya haɗa manoma da kuma yan su, wato sna'ar kamun kifi, kuma kauyen yana a yankin Nijar, na tafkin Chadi a ƙaramar hukumar Monguno.

Ahmadu ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun jima basu kai hari ƙauyen ba, domin idan ma sun shigo ƙauyukan dake yankin abinci kawai suke ɗiba.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Har zuwa yanzun sashin watsa labarai da hulɗa da jama'a na rundunar sojojin sama bai ce komai ba game da wannan lamarin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wani labarin na daban Kotu ta tsige dan majalisar tarayya na jam'iyyar APC daga kujerararsa

Wata kotun tarayya dake zamanta a Jalingo, jihar Taraba, ta tsige ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bali/Gasol, Hon. Mubarak Gambo.

Kotun ta umarci INEC ta kwace shaidar zaɓe daga hannun tsohon ɗan majalisar ta baiwa wanda bincike ya gano shine ya taka takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262