Ana jita-jitar Jonathan zai koma APC, sai ga PDP ta nemi ganawa dashi kan wani batu

Ana jita-jitar Jonathan zai koma APC, sai ga PDP ta nemi ganawa dashi kan wani batu

  • A yayin da ake tunanin Goodluck Jonathan zai koma APC, PDP ta ambace shi a matsayin mayan jam'iyya
  • PDP ta ce za ta tuntube Jonathan yayin da take shirin kaddamar da babban taron jam'iyya a watan gobe
  • Hakazalika, PDP ta magantu kan batun tuntubar shugaban ta da aka dakatar, Uche Secondus

Makwannin da suka gabata an samu rahotannin da ke cewa jam'iyyar APC na zawarcin tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonatha, amma PDP ta fito ta yi bayanin gaskiyar lamari.

Wani rahoton The Guardian ya ce, Kwamitin Babban Taron Jam’iyyar PDP, ya lissafa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, a cikin shugabannin jam’iyyar da za su tuntuba kafin babban taron da za a yi ranar 30 zuwa 31 ga Oktoba.

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, wanda mataimakinsa, Haruna Manu, ya wakilce shi a taron kaddamar da kwamitin, shi ya ba da wannan bayanin, a Abuja ranar Talata 28 ga watan Satumba.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Ana jita-jitar Jonathan zai koma APC, sai ga PDP su nemi ganawa dashi kan wani batu
Taron Jam'iyyar PDP | Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

A rahoton da Punch ta fitar ta ce, da yake amsa tambaya kan batun, Manu ya ce:

“Ina tabbatar muku da cewa duk wadanda suka ambata cewa za a tuntube su za a tuntube su.
Kuma idan tsohon shugaban kasa (Jonathan) yana cikin mutanen da ya kamata a tuntube su, ina tabbatar muku da cewa za a tuntube shi.”

Ya yi bayanin cewa kwamitin ya hadu ne don karban bayanai daga mambobi kan hanyoyin da za a bi don cimma burin da aka sa a gaba na shirya kasafin kudi wanda za a gabatar wa babban kwamiti don amincewa da wucewa gaba.

Manu ya ci gaba da cewa:

“Wannan muhimmin kwamiti na tuntuba da tattarawa yana yin taro ne a yau don tattauna hanyoyi, kan yadda za mu gudanar da ayyukanmu da dawainiyarmu.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

"Kuma wannan shine ainihin abin da muka yi. Bayan yau, za mu fito da kasafin kudin mu, abin da muke bukata na babban taro. Wannan shine ainihin abin da muka tattauna.”

Shin za a tuntubi shugaban PDP Uche Secondus?

Da aka tambaye shi ko kwamitin na tuntubar Shugaban PDP na kasa da aka dakatar, Uche Secondus, Manu ya ce:

“An yi wannan tambayar a makon da ya gabata kuma shugaban kwamitin taron ya amsa muku kan hakan. Don haka, amsata har yanzu ita ce abin da shugaban wannan kwamiti mai mahimmanci ya fada.”

Shugaban kwamitin taron kuma gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, yayin da yake amsa tambaya kan batun Uche Secondus a makon da ya gabata, ya ce:

“Har sai kotu ta yanke hukunci kan Secondus, ina ganin matsayin da ake ciki na cewa dattijo Yemi Akinwonmi ne zai shugabanci babban taron.”

Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja

Read also

Ba mu ci ta zama ba: 'Yan sanda sun dukufa a aikin ceto wani babban soja da aka sace

A wani labarin, majalisar dattijai a ranar Talata ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da Naira biliyan 300 a matsayin kudin taimakon gaggawa don gyara munanan hanyoyi a jihar Neja.

Wannan kuduri na babban zauren ya biyo bayan wani kudiri kan lalacewar hanyoyi a fadin jihar Neja da toshe hanyoyin ta hanyar nuna rashin amincewa da direbobin tirela da direbobin tanka suke yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Mataimakin Babban Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abudullahi, mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudirin, in ji rahoton The Nation.

Source: Legit.ng

Online view pixel