'Yan sanda sun dakile yunkurin sace mutane, sun cafke wanda ake zargi a Kano
- Hukumar 'yan sandan jihar Kano ta yi nasarar dakile wani yunkuri na garkuwa da mutane a kauyen Danzabuwa, da ke karamar hukumar Bichi
- Hakan ya kasance ne bayan ta samu korafi daga wani mutum cewa an yi masara barazana na biya wasu kudade ko kuma a sace shi ko wani daga cikin iyalinsa
- Bayan bincike an gano wani daga cikin danginsa ne ke masa barazanar inda aka kamo shi
Rundunar 'Yan sanda a jihar Kano ta dakile yunkurin sace mutane a kauyen Danzabuwa, da ke karamar hukumar Bichi.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa kakakin rundunar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce wannan ya biyo bayan korafin da wani mazaunin Kauyen Danzabuwa, Karamar Hukumar Bichi, Jihar Kano ya shigar, cewa an tuntube shi ta waya kuma an yi masa barazanar biyan Naira miliyan daya ko kuma a sace shi ko daya daga cikin ‘ya’yansa.
Kiyawa ya ce bayan korafin, 'yan sanda sun shiga aiki kuma sun yi nasarar cafke Tukur Ahmad mai shekaru 28, a Kauyen Panda, Karamar Hukumar Keffi, Jihar Nassarawa a ranar Asabar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce wanda ake zargi wanda dangin mai karar ne ya amsa laifinsa kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu don hukunta shi.
Rundunar, duk da haka, ta ba da tabbacin ci gaba da jajircewa wajen samar da yanayin zaman lafiya a jihar.
Rahoton ya kara da cewa rundunar ta kuma bukaci jama'a da su baiwa 'yan sanda duk wani muhimmin bayani da zai taimaka wajen kiyaye tsaron jihar.
Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara, sun fitittiki kowa
A wani labari na daban, wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari hedkwatar karamar hukumar Rafi a jihar Neja kuma sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Kagara.
An ce yan bindiga sun dira fadar ne cikin babura 20 dauke da yan bindiga uku-uku.
Thisday ta ruwaito cewa wani babban mai mukami a fadar ya bayyana cewa Allah ya taimaka Sarkin ba ya gari.
Asali: Legit.ng