Katsina: Idan kika tona min asiri, ba za ki taɓa gama jami’ar nan ba, Shugaban UMYUK ga wata budurwarsa
- Shugaban jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke jihar Katsina, Farfesa Sunusi Mamman ya yi barazanar hana budurwar sa kammala jami’ar
- Ya bukaci kada ta nuna ta san sa yayin da ake bincike akan sa bisa zargin amfani da matsayin sa wurin harkokin da basu dace ba da daliban sa mata
- A wani sako da ya yi wa wata budurwarsa, Aisha Tahir, ta WhatsApp ya ce matsawar tana so ta gama makarantar ta rufe bakin ta
Jihar Katsina - Shugaban jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke Jihar Katsina, Farfesa Sanusi Mamman ya yi barzanar korar budurwarsa daga jami’ar idan har ta nuna ta san shi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ana zargin Mamman, wanda yanzu haka farfesa ne a bangaren ilimi na musamman, da laifuka masu yawa tun daga wadaka da dukiyar makarantar zuwa yin harkokin da basu dace ba da wasu dalibansa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An zarge shi da gyara wa daliban sa da suka koma ‘yan matan sa sakamakon jarabawar su da sauran su.
Yakan sa a dauke wuta idan zai kai wa ‘yan matan sa ziyara a makwancin su na makarantar
Ana zargin VC din da bayar da umarnin a dauke wuta a gaba daya makwancin dalibai mata idan zai kai wa budurwar sa ziyara.
Bayan korafin jama’a ya yawaita, har da na tsofaffin daliban sa, Daily Nigerian ta tattaro bayanai akan yadda hukumar makarantar ta shirya wata kungiya da zata yi bincike akan wannan zargin da ake ma sa.
Sai dai kungiyar ta gayyaci wasu daga cikin daliban sa don su bayar da shaida akan sa, daga nan ne Mamman ya rude ya fara kiran tsofaffin ‘yan matan sa yana razana su akan kada su tona masa asiri.
Aisha Tahir, daya daga cikin ‘yan matan sa ta tattauna da Daily Nigerian ta wayar salula inda ta ce VC din ya yi barazanar hana ta kammala makarantar matsawar ta fallasa ma sa asiri.
Ya ce kada ta kuskura ta nuna ta san shi
Kamar yadda ta bayyana ya tura mata sako ta WhatsApp:
“Ki dage akan cewa mahaifin ki ne ya biya miki kudin dakin da kike zama a makaranta. Idan ki ka yi wani kuskure, za ki rasa digirin ki.
“Ki sanar da su cewa sunan da ake kiran ki, ‘First Lady’ dama tsohon suna ne kuma baki sanni ba gaba daya.”
Aisha daliba ce ‘yar aji 4 a jami’ar inda take karanta Geography Education. Dalibai ne su ka sa mata suna First Lady. Ta ce razanar da ita da VC din ya yi ne yasa ta ce sai ta tona ma sa asiri.
A cewarta, VC din ya nemi auren ta don har Malumfashi ya je wurin iyayen ta ya nemi auren ta da kudi N110,000 a matsayin kudin na-gani-ina-so da kuma sadaki.
Ta ce:
“Da farko ya neme ni ta Facebook ne inda ya bukaci in ba shi lambar waya ta. Ban gane shi ba, na zaci kawai wani ne daban, sai ya ce min shi malami na ne ya tura min hoton sa.
“Bayan nan ne mu ka fara magana, sai dai daga baya ya fara korafi akan yadda na sanar da mutane soyayyar mu.
“Na yi kokarin gamsar da shi cewa batun aure babu sirri kuma ko ban bayyana ba, ‘yan uwa na da ya samu a Malumfashi za su bayyana.
“Daga nan ne muka rabu. Ya dakatar da lambata daga kiran sa sannan muka dena magana gaba daya har sai yanzu da maganar nan ta taso.
“Mahaifi na ya fara kira ya bukaci in yi karya a gaban hukumar makarantar dake bincike akan sa. Ya tsoratar da shi akan cewa in har na fadi gaskiya ba zan gama jami’ar nan ba.”
An yi kokarin jin ta bakin VC din amma lambarsa ba ta zuwa kuma bai bayar da amsar sakon da Daily Nigerian ta tura ma sa ba dangane da zargin.
Asali: Legit.ng