Makasan mijin Dora Akunyili za su fuskanci hukuncin duniya da na Ubangiji, Buhari

Makasan mijin Dora Akunyili za su fuskanci hukuncin duniya da na Ubangiji, Buhari

  • Shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan uwan wadanda su ka rasa rayukansu su a harin da ya janyo kisan Dr Chike Akunyili cewa za a dauki mataki
  • Kamar yadda shugaban kasar ya tabbatar mu su, duk wadanda suke da alhakin kisan za su fuskanci hukunci a duniya da lahira
  • Shugaban kasar ya bayar da wannan tabbacin ne ta wata takarda wacce kakakin sa, Femi Adesina ya gabatar

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa da ‘yan uwan wadanda su ka rasa rayukan su a farmakin da ya yi sanadin mutuwar Dr Chike Akunyili cewa, duk masu alhakin kai farmakin za su fuskanci hukunci a nan da lahira.

Shugaban kasan ya bayar da wannan tabbacin ne ta wata takarda ta ranar Laraba wacce kakakin sa, Femi Adesina ya saki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An cafke wani sojan karya da abokinsa da ke samar wa da 'yan bindiga hanyoyin sadarwa

Makasan mijin Dora Akunyili za su fuskanci hukuncin duniya da na Ubangiji, Buhari
Makasan mijin Dora Akunyili za su fuskanci hukuncin duniya da na Ubangiji, Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, ya bukaci jami’an tsaro da shugabanni su hada kai wurin aiki tukuru don kawo karshen ta’addancin da ke cutar da ‘yan Najeriyan da ba su ji ba basu gani ba.

Buhari ya bayyana takaicin sa dangane da kisan gillar da aka yi wa Dr Chike, mijin tsohon darekta janar na hukumar kula da ingancin abinci da kwayoyi, NAFDAC, Farfesa Dora Akunyili.

A cewar Adesina, shugaban kasar ya bayyana radadin da yaran farfesan da Dr Akunyili da iyalan sa har da abokan arziki wadanda rayuwar su ba za ta taba kasancewa kamar da ba sakamakon zalunci da kisan rashin mutunci da ya auku a Onitsha da ke jihar Anambra.

“Shugaban kasa Buhari ya na tuna lokacin da yake aiki tare da Dora Akunyili a PTF kuma ‘yan Najeriya ba za su taba manta lokacin amazon ba, wanda ita kan ta Akunyili mace ce mai kwazo da kishin kasa,” kamar yadda takardar ta bayyana.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

Rahoto: Yadda datse layikan sadarwa ke barazana ga kasuwanci a arewa maso yamma

A wani labari na daban, kasuwanci ne a halin yanzu ke jin tsanani kan hukuncin gwamnati na datse layikan sadarwa a wasu jihohin arewa maso yamma na kasar nan kamar yadda rahotannin SB Morgan suka bayyana, TheCable ta ruwaito.

Rahotan mai taken; "Hostile reception - The impact of telephony shutdowns in North-West Nigeria," wanda aka bincike mutum 679 a makon tsakiyan watan Satumban 2021 domin duba abinda datse kafofin sadarwa suka janyo.

A ranar 3 ga watan Satumba, an bukaci hukumar sadarwa da ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin datse sabis a Zamfara domin shawo kan miyagun al'amuran 'yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel