Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara, sun fitittiki kowa

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara, sun fitittiki kowa

  • Bayan wata daya da sako daliban Tegina, yan bindiga sun sake kai hari Neja
  • Sun far wa fadar Sarkin Kagara amma an ci sa'a mai martaba ya yi tafiya
  • Gwamnatin jihar ta katse layukan waya a yankin don jami'an tsaro

Neja - Wasu tsagerun yan bindiga sun kai hari hedkwatar karamar hukumar Rafi a jihar Neja kuma sun kai farmaki fadar mai martaba Sarkin Kagara.

An ce yan bindiga sun dira fadar ne cikin babura 20 dauke da yan bindiga uku-uku.

Thisday ta ruwaito cewa wani babban mai mukami a fadar ya bayyana cewa Allah ya taimaka Sarkin ba ya gari.

Yace:

"Mun yi sa'a Sarkin baya gari, ya fada min zai yi tafiya."

An samu labarin cewa Sarkin ya tafi birnin jihar Minna domin halartan bikin yaye dalibai a makarantar New Gate College of Technology.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yanzu dai babu labarin o an kashe wani a harin saboda an katse layukan sadarwa a yankin domin taimakawa jami'an tsaro wajen aiki.

Wannan abu na faruwa ne wata daya bayan garkuwa da daliban makarantar Islamiyyan Salihu Tanko.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara, sun fitittiki kowa
Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Kagara, sun fitittiki kowa
Source: Original

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

A ranar 26 ag Agusta, sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata.

An sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Source: Legit.ng

Online view pixel