Rundunar sojin ruwa ta nesanta kanta da jami’ar da ta zargi sojojin Chadi da sayar da makamai
- Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta nesanta kanta da wasu kalamai da wata babbar jami'arta ta gabatar a gaban kwamitin tsaro na majalisar wakilai
- Babbar jami'ar mai suna Kwamado Jamila Sadiq Abubakar, ta zargi sojojin kasar Chadi da saida kananan makamai idan suka rasa kudin kashewa
- Sai dai kuma, rundunar sojin, a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Talata, ta ce ba da yawunta jami'ar ta furta wadannan kalamai ba, domin ra'ayinta ne kashin kanta
Abuja - Rundunar sojin ruwan Najeriya ta nesanta kanta da Kwamado Jamila Sadiq Abubakar, wacce ta zargi sojojin Chadi da sayar da makamai ba bisa ka’ida ba, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Abubakar ta yi wannan zargin ne a wani taron jin ra'ayin jama'a da kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya.
Yayin da take ba da gudummawa ga kudirin da ke neman kafa Hukumar Kasa ta Yaki da Kananan Makamai, Abubakar ta ce makaman da kasashen da suka ci gaba suke ba kasashen makwabta suna "kara" kalubalen tsaro na Najeriya.
Ta yi zargin cewa sojojin kasashen da ke makwabta na sayar da makamansu idan suka shiga matsala ta rashin kudi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar ta ruwaito cewa a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 28 ga watan Satumba, Suleman Dahun, mai magana da yawun rundunar sojojin ruwan Najeriya, ya ce ra’ayin jami’ar bai yi daidai da matsayin rundunar sojin ruwan ba.
Sanarwar ta ce:
“Kwamitin Majalisar Wakilai kan Tsaro da Leken Asiri na Kasa a jiya 27 ga watan Satumba, 2021 ya gudanar da zaman sauraron ra'ayoyin jama'a kan wasu Kudurai 4 da suka hada da na kafa Hukumar Kasa kan yakar yaduwar kananan makamai (HB 10). A yayin sauraron wannan doka, wakiliyar Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya (NN) ta gabatar da kalamai na kashin kanta ba tare da yawun rundunar ba kan batun fataucin kananan makamai.
“Lamarin ya shafi alakarmu da kasashe da ke makwabtaka wadanda muke da kyakkyawar fahimta da su, kuma ra’ayin ya saba da na rundunarmu.
“Rundunar sojin ruwa na nesanta kanta da ra’ayin wannan babbar jami’ar. Muna jinjina wa gudunmawar da makwabtan kasashe suke bayarwa wajen yaki da yaduwar kanana da matsakaitan makamai.”
An fadawa Majalisa Yadda Sojojin Chadi ke saida makamansu araha banza idan sun rasa kudi
A baya mun ji cewa rundunar sojojin ruwan Najeriya ta zargi sojojin kasar Chadi da laifin saida kananan makamai ta hanyar da ba ta dace ba.
Shugaban hafsun sojan ruwa na kasar nan, Awwal Gambo ya bayyana wannan a lokacin da ya bayyana a gaban zauren majalisar wakilan tarayya.
Commodore Jemila Abubakar tayi wannan bayani da ta wakilci shugaban hafsun sojin ruwan wajen sauraron wasu kudiri da aka gabatar a majalisa.
Asali: Legit.ng