An fadawa Majalisa Yadda Sojojin Chadi ke saida makamansu araha banza idan sun rasa kudi

An fadawa Majalisa Yadda Sojojin Chadi ke saida makamansu araha banza idan sun rasa kudi

  • Shugaban hafsun sojan ruwa ya zargi sojojin wasu kasashe da saida makamai
  • Awwal Gambo ya yi wannan bayani a lokacin da ya bayyana a zauren majalisa
  • Gambo yace sojojin Chadi na saida makamai a kan $20 idan suna neman kudi

FCT, Abuja Daily Trust tace rundunar sojojin ruwan Najeriya ta zargi sojojin kasar Chadi da laifin saida kananan makamai ta hanyar da ba ta dace ba.

Shugaban hafsun sojan ruwa na kasar nan, Awwal Gambo ya bayyana wannan a lokacin da ya bayyana a gaban zauren majalisar wakilan tarayya.

Commodore Jemila Abubakar tayi wannan bayani da ta wakilci shugaban hafsun sojin ruwan wajen sauraron wasu kudiri da aka gabatar a majalisa.

Jaridar tace ‘yan majalisar tarayya sun kawo wasu kudirori da ake sa rai za su takaita yaduwar kananan makamai a Najeriya domin samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Jemila Abubakar ta shaida wa majalisar wakilan cewa makaman da suke yawo a wasu kasashe suna kawo masu cikas wajen yakar matsalar rashin tsaro.

Sojojin Chadi
Rundunar Sojojin Chadi Hoto: www.thedefensepost.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me Commodore Jemila Abubakar ta fada wa Majalisa?

“Na jagoranci yakin Boko Haram, kuma zan iya fada maku cewa wasu kasashe ba su da gidan makamai.”
“Ba su da gidajen makamai, saboda haka ana ba su gudumuwar makamai ne. Bana so in fadi sunayen kasashen – Amma kasashe masu taso wa da suke taimaka mana, suna kara kawo mana cikas a Najeriya.”
“Saboda za ka ga sojan Chad yana da makamai 20 zuwa 30 a karkashin gadonsa. Da zarar ya rasa kudi, sai ya fito da su ya saida a kan $20 ko $30.”

Da take jawabi, Commodore Jemila Abubakar tace akwai bukatar a hada-kai da ECOWAS domin a kawo dokar yadda za a rika amfani da makamai a Afrika.

Kara karanta wannan

ASUU: Malaman Jami’a za su hadu da Gwamnati a kan yiwuwar sake shiga yajin-aiki

Idan zargin da babbar jami’ar sojar ta Najeriya ta jefi sojojin kasar Chadi sun tabbata, farashin abin da ake saida bindiga a makwabtan bai wuce N12, 000 ba.

Dazu aka ji Dan Majalisar tarayya, Babajimi Benson yace an ba jami’an tsaro lokaci su kawo karshen aika-aikan 'yan ta'adda da 'yan bindigan a Najeriya.

Hon. Babajimi Benson ya soki afuwar da ake yi wa sojojin Boko Haram, yace kyau a kashe su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel