2023: Arewa za ta tashi da tikitin shugaban kasa a PDP, Yarbawa da Shugaban Jam'iyya

2023: Arewa za ta tashi da tikitin shugaban kasa a PDP, Yarbawa da Shugaban Jam'iyya

  • Akwai alamu cewa ‘Dan Arewa zai rike wa PDP tuta a babban zaben 2023
  • Kafin nan za a ba Kudu maso yamma kujerar shugaban jam’iyya na kasa
  • Ana rade-radi Gwamnan jihar Oyo yana goyon bayan Ọlagunsoye Oyinlọla

Abuja - Yayin da ake shirin zaben sababbin shugabannin jam’iyyar PDP na kasa, ‘yan siyasar Kudu maso yamma suna neman kujerar shugaban jam’iyya.

Jaridar Daily Trust tace jam’iyyar PDP za ta tsaida wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023 ne daga jihohin yankin Arewacin Najeriya.

Haka zalika jam’iyyar adawar za ta fito da shugabanta na kasa daga cikin jihohin kudancin kasar nan.

Su wanene ke neman kujerar Secondus?

Kusoshin PDP na Kudu maso yamma sun kwallafa ransu a kan kujera, daga cikinsu akwai; Bode George; tsohon ‘dan takarar gwamnan Ondo, Eyitayo Jegede.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

Sai kuma Jimi Agbaje da Ọlagunsoye Oyinlọla. Daga baya-bayan nan kuma an ji cewa tsohon gwaman Ekiti, Ayodele Fayose yana neman wannan kujerar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam'iyyar PDP
Gangamin PDP a Edo Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Zuwa yanzu akwai mutane daga kowace jiha da ke neman zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

A makon da ya gabata jam’iyyar PDP ta nada kwamitin karba-karba, wanda zai fito da yadda za a ware tikiti da kuma yankin da ya kamata a ba kowane mukami.

Rahoton yace idan kwamitin na Ifeanyi Ugwuanyi ya zauna, zai ware kujerar zuwa yankin Yarbawa domin su rage fushin abin da ya faru da su a zaben 2017.

Gwamna na goyon bayan Ọlagunsoye Oyinlọla

Wani daga cikin dattawan PDP a Legas, Dr. Layi Ogunbambi, yace idan za a kamanta gaskiya, ayi adalci, yankin Kudu maso yamma za a ba kujerar shugaban PDP.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hon. Elumelu ya bayyana Gwamnan da zai iya hambarar da APC daga kan mulki

Dayo Ogungbenro wanda yana cikin manyan PDP yace gwamnan Oyo, Seyi Makinde yana goyon bayan Olagunsoye Oyinlola ya zama sabon shugaban PDP na kasa.

Kawo yanzu PDP ba ta yi magana a kan yadda za tayi rabon mukamai da tikiti zuwa 2023 ba.

Za a kori wasu 'yan APC

A makon nan aka ji uwar Jam’iyyar APC za ta dauki mataki mai tsauri, za ta hukunta masu saba umarnin da NEC ta bada na cewa a janye duk wata kara a kotu.

Wasu ‘ya ‘yan jam’iyya suna kai APC kotu duk majalisar NEC tace ayi sulhu a cikin gida. Alamu sun nuna cewa za a fara yin waje da masu kunnen-kashi a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel