Miyagun Yan bindiga sun yi awon gaba da Kansila, karo na uku cikin mako 3
- Rundunar yan sanda reshen jihar Akwa Ibom, ta tabbatar da sace kansilan gunduma ta 6 dake ƙaramar hukumar Eket
- Rahotanni sun bayyana cewa wannan shine karo na uku a cikin makonni uku ana aikata masa haka
- Kwamishinan yan sandan jihar, Andrew Amiengheme, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin sace kansilan
Akwa Ibom - Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace kansilan guduma ta 6 a ƙaramar hukumar Eket, jihar Akwa Ibom, ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kakakin yan sandan jihar, SP Odiko Macdon, shine ya tabbatar da faruwar harin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Eket.
Yace maharan sun sace kansilan ne a harabar gidan mai ranar Asabar, 25 ga watan Satumba, da misalin karfe 8:00 na dare.
Kwamishina ya bada umarnin bincike
Macdon ya bayyana sace kansilan da babban abun takaici kuma hukumar yan sanda ba zata lamurta ba, yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kwamishinan yan sanda, Andrew Amiengheme, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin."
"Tabbas mun samu rahoto, kuma mun fara aiki kan lamarin, bincike ya yi nisa kuma ba zan ɓoye gaskiya kan cewa muna da masaniya a lamarin ba."
"Binciken mu ya yi nisa sosai kuma ba tare da jimawa ba zamu ceto shi. Bana son fallasa abubuwan da binciken mu ya gano domin tabbatar da mun cimma nasara."
Yan sanda zasu tabbatar da kamo maharan
Kakakin yan sandan ya tabbatar da cewa hukumarsu zata yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da an hukunta waɗanda suka aikata garkuwa da kansilan, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A wani labarin na daban Babu ranar daina satar jarabawa a Arewa sai an yi abubuwa biyu, Farfesa Salisu Shehu
Shugaban jami'ar Al-Istiqama dake Sumaila jihar Kano, Farfesa Salisu Shehu, yace babu ranar daina magudin jarabawa a arewa har sai an ɗauki matakai biyu.
A wata fira da ya yi da wakilin mu na Legit.ng Hausa, Farfesan yace ainihin abinda ke kara rura wutar satar jarabawa a Arewa shine rashin tsoron Allah da lalacewar al'umma.
Asali: Legit.ng