Ana tsaka da taro, tsagerun yan bindiga sun buɗe wuta kan mambobin jam'iyyar APC

Ana tsaka da taro, tsagerun yan bindiga sun buɗe wuta kan mambobin jam'iyyar APC

  • Wasu miyagun yan bindiga sun buɗe wuta kan mambobin jam'iyyar APC suna cikin gudanar da taro a jihar Anambra
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun jikkata mahalarta taron, yayin da likita ya tabbatar da mutum ɗaya ya mutu a asibiti
  • Kakakin rundunar yan sanda, DSP Toochukwu Ikenga, yace kwamishina ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin

Anambra - Rahotanni sun bayyana cewa ranar Lahadi, wasu miyagun yan bindiga sun kai hari kan mambobin APC a ƙaramar hukumar Nnewi, jihar Anambra, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

This day ta gano cewa mambobin APC na tsaka da taro a gundumar Uruagu, a shirin da suke na tunkarar zaɓen gwamna, kwatsam yan bindiga suka buɗe musu wuta.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

Harin da miyagun suka kai yayi sanadiyyar mutuwar ɗaya daga cikin mambobin mai suna, Somadina Oforma.

Yan bindiga sun kai hari kan mambobin APC
Ana tsaka da taro, tsagerun yan bindiga sun buɗe wuta kan mambobin jam'iyyar APC Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakanan kuma rahotanni sun tattaro cewa wasu mahalarta taron da dama sun jikkata, sanadiyyar harin yan bindigan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Anambra, DSP Toochukwu Ikenga, ya tabbatar da kai harin da cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:00 na daren ranar Lahadi.

Kakakin yan sandan yace:

"Kwamishinan yan sanda, reshen jihar Anambra, CP Tony Olofu, ya bada umarnin aiwatar da bincike kan harin da aka kai Uruagu, ƙaramar hukumar Nnewi, ranar 26 ga watan Satumba."
"Rahoton binciken mu ya nuna cewa wasu mahara sun farmaki yankin Uruagu, da misalin ƙarfe 7:00 na dare, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sanata tare da dubbannin mambobin PDP sun sauya sheka zuwa APC mai mulki

"An yi gaggawar kai mutun biyu da suka samu raunuka zuwa Asibiti, amma likita ya tabbatar da ɗaya daga cikinsu mai suna, Mr Somuadina Oforma, ya mutu."

A wani labarin kuma Shugaban ƙungiyar gwamnoni kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yace ya bar lamarinsa a hannun Allah game da zaɓen 2023

Gwamnan yace babu wanda yasan abinda Allah ya tanazar masa a motsin siyasarsa na gaba yayin da babban zaɓe ke kusantowa.

Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake martani kan fastocina da aka watsa na takarar shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: