Takarar shugaban ƙasa a 2023: Allah kadai yasan abinda ya tanazar mun a gaba, Gwamna ya magantu
- Shugaban ƙungiyar gwamnoni kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yace ya bar lamarinsa a hannun Allah game da zaɓen 2023
- Gwamnan yace babu wanda yasan abinda Allah ya tanazar masa a motsin siyasarsa na gaba yayin da babban zaɓe ke kusantowa
- Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yake martani kan fastocinsa da aka watsa na takarar shugaban ƙasa
Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, kuma shugaban ƙungiyar gwamnoni (NGF), Kayode Fayemi, yace Allah kaɗai yasan abinda ya tanazar masa nan gaba a siyasar 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Fayemi ya yi wannan furuci ne ranar Lahadi, yayin da yake fira da kafar watsa labarai ta Arise TV.
Meyasa Gwamnan ya yi wannan magana?
Tuna watan Agusta, 2020, fastocin yaƙin neamn zaɓen shugaban ƙasa na gwamna Fayemi suka watsu, kuma hakan ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Wanda ya ɗauki nauyin buga fastocin kuma ciyaman na ƙaramar hukumar Ikere ta jihar Ekiti, Femi Ayodele, yace ya yi haka ne domin nuna goyon bayansa ga Fayemi.
Bugu da ƙari Ayodele ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin maida martani ga masu yaɗa jita-jitar cewa yana cin dunduniyar gwamnansa.
Akwai babban aiki a gabana - Fayemi
Amma da aka tambaye shi ranar Lahadi kan ko yana da shirin neman tikin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023, Fayemi yace:
"Ina da aiki a gabana, ina fatan gama mulkin jihar Ekiti lami lafiya. A yanzun jihar Ekiti nasa a gaba wajen ganin na kawo mata cigaba a ragowar lokacin da nake da shi a Ofis."
"Allah kaɗai yasan abinda zai faru nan gaba, amma zamu keta duk inda ya dace idan muka isa can. A halin yanzu jihar Ekiti ce a gabana."
Wace jam'iyya zata lashe zaɓen 2023?
Gwamna Fayemi ya yi hasashen cewa jam'iyyarsa ta APC ce zata sake ɗarewa madafun iko a babban zaɓen 2023 dake tafe.
Yace:
"Muna da yaƙinin APC zata sake lashe zaɓen 2023, amma kafin nan yanzun mun maida hankali ne kan ƙasa. Gwamnatin APC ta fi maida hankali wajen saita Najeriya da samar da tsaro."
"Amma abinda ke faruwa a cikin jam'iyyar APC wani abu ne da ya shafi mambobinta kaɗai, kuma abu ne da zamu sulhunta shi a tsakanin mu."
A wani labarin kuma Tsohon mataimakin gwamna tare da jiga-jigan APC 15 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
Jam'iyya mai mulkin ƙasar nan ta samu koma baya a jihar Gombe, yayin da jiga-jiganta aƙalla 15 suka koma jam'iyyar PDP.
Tsohon mataimakin gwamnan Gombe, Lazarus Yoriyo, yace sun ɗauki matakin ficewa daga APC ne saboda abinda ke faruwa a ciki.
Asali: Legit.ng