Sarkin Musulmi: Almajiranci Da Yawon Barace-Barace a Tituna Ba Musulunci Bane

Sarkin Musulmi: Almajiranci Da Yawon Barace-Barace a Tituna Ba Musulunci Bane

  • Sarkin musulmi na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira akan amfani da ilimin addini da na boko wurin kawo karshen almajiranci a arewa
  • Ya yi wannan jawabin ne a wani taro da suka yi a karshen mako wanda su ka tattauna akan hanyoyin inganta ilimin almajirci a jihar Sokoto
  • A cewar Sarkin, wajibi ne a taru a hada kai wurin kawo karshen barace-barace a titunan jihar Sokoto da arewacin Najeriya

Sokoto - Sarkin musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira akan amfani da ilimin addinin musulunci da na zamani wurin kawo karshen almajirci a arewacin Najeriya.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ya yi wannan jawabin ne a ranar kammala wani taro da suka kwashe kwana 2 suna yi akan hanyoyin inganta ilimin Almajirci a jihar Sokoto.

Read also

Kungiyar CAN Ta Karrama Wani Limami Akan Ceton Kiristoci 200 Da Ya Yi a Plateau

Sarkin Musulmi: Almajiranci Da Yawon Barace-Barace a Tituna Ba Musulunci Bane
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Nation
Source: Facebook

Abubakar ya ce wajibi ne masarautar da sauran su hada kai wurin kawo ci gaba wanda zai kawo karshen barace-barace a jihar Sokoto da arewacin Najeriya gabadaya.

Basaraken ya yi jawabin inda ya ce shi da sauran mutane da dama sun yi ilimin almajirci saidai sun yi shi ne don neman ilimin addini da larabci ba bara ba.

Sarkin musulmi ya ce wajibi ne iyaye su dage wurin hana yaran su bara

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ya ce:

“Wajibi ne iyaye su tsaya tsayin daka wurin hana yaransu bara. Ko da mu ka je makarantar allo, ba a aike mu bara ba face neman ilimi.”

Abubakar ya ce wajibi ne a taru a yi hani da al’adar bara. Yayin da yake yaba wa kokarin gwamnatin tarayya wurin taimako ga jama’a, sarkin ya yi kira ga gwamnati wurin sanya kudaden da suka dace wurin inganta ilimi a Najeriya ta hanyar jihohi da kafafen da su ka dace.

Read also

Aikin wutan da ya yi sanadiyyar mutuwar Abba Kyari ya tsaya cak bayan an sa hannu

Kamar yadda ya ce:

“Ayi kokarin samar da kudade ga jihohi ta yadda za a inganta ilimi da sauri. Babu abinda ya kai kudi kawo saurin aiki. Don haka idan kowa ya wadata da ilimi, abubuwa da dama za su gyaru.”

Gwamna Tambuwal ya ce taron zai samar da nasara

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana taron a matsayin hanyar samar da nasara. A cewar sa mulkin sa zai taimaka wurin bunkasa ilimi.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito ya ce:

“Dalilin mu na wannan taron shi ne musamman don kawo hanyoyin da zasu yi gaggawar samar da mafita ne. Ina so in yi godiya ga UNICEF Intervention programme a wurin fannin ilimi a jihar Sokoto. Gwamnatin jihar za ta samar da kwamiti da za ta zama karkashin shugabancin Malam Lawal Maidoki don kawo canji.”

Sakataren kungiyar ilimin larabci da dana musulunci na jihar Sokoto, Dr Umar Aliyu Dandin Mahe, ya ce wannan salon zai dace da salon Indonesia Pondok na gyara ga salon Almajirci.

Read also

Ku daina tsinewa shugabanninku saboda wahalar rayuwa – Sanusi ga ‘yan Najeriya

Ya ce ya kai shekara daya da rabi da jihar ta fara bin irin wannan salon.

Sultan: Allah bai yi kuskure ba da ya haɗa mu zama tare a matsayin ƴan Nigeria

A wani labarin, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar na III, ya bukaci dukkan kabilun Nigeria su cigaba da zama a matsayin yan uwan juna domin Allah bai yi kuskure ba da ya hada mu zama a matsayin kasa daya, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke jawabi a matsayinsa na shugaba a wurin taron bada lambar yabo na shugabanci na 2020 a ranr Alhamis a Abuja, Sultan ya ce raba kasar ba zai magance matsalolin da kowace kabilar ke fama da shi ba amma hada kai tare a warware matsalar ce ta fi amfani.

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel