El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan

  • Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce yankin arewa maso yamma na kasar nan ya na cikin matsanancin rikici
  • Gwamnan ya kwatanta halin da yankin ya fada da yanayin halin da kasar Afghanistan ta fada na rikici
  • Ya bayyana yadda rashin tsaro ya ke shafar fannonin da suka hada da ilimi da kuma lafiya, lamarin da ke kara tada hankali

Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce kiyasin da ake a halin yanzu da ake yi a arewa maso yamma ya na kai da kai da yadda Afghanistan ta fada rikici, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamnan ya sanar da hakan a ranar Talata a wani taro wanda aka yi masa take da “Human Capital Development Communications Strategy Validation Meeting” wanda majalisar kula da tattalin arzikin kasa mai samun shugabancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ta shirya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Masari: Muna cin nasara kan 'yan bindiga, sojoji na gasa musu aya a hannu

El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan
El-Rufai: Arewa maso yamma ta rikice, kiyasin mu ya na kai da kai da Afghanistan. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ba gwamnan jihar Kaduna ba kadai, karamin ministan ilimi, Chukwemeka Nwajiuba, ya yi jawabi a wurin taron, Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya ce ba yanayin tsarin shugabanci na siyasa ne kadai zai ture irin yanayin Afghanistan da ya tunkaro mu, a kara da zuba manyan hannayen jari da bangaren ilimi na kasar nan domin shawo kan matsalar 'yan fashin daji, ta'addanci, garkuwa da mutane da sauran matsaloli.

Ya ce:

"Ina wakiltar yankin arewa maso yammaci kuma kun san yankinmu ya matukar fadawa cikin matsalar yawan yara da basu zuwa makaranta. Mu ke da yawan talauci da kuma yawan yaran da ke barin makaranta."
"Kamar hakan bai isa ba, da yawa daga cikin makarantun mu an rufe su saboda matsalar rashin tsaro a makarantun kwanan mu. A jihohi masu tarin yawa na arewa maso yamma, an rufe makarantu na wani lokaci saboda aiki da jami'an tsaro ke yi, hakan ya kara lalata fannin ilimi.

Kara karanta wannan

Fitaccen Sanatan APC ya nuna damuwa kan yadda majalisa ke saurin amincewa Buhari ya ciyo bashi

“A bangaren lafiya duk zancen daya ne. Saboda haka ne za ka ga arewa maso yamma ce ta ke da mafi yawan gwamnoni da mataimakansu da suka halarci taron nan.
"Babban yayana, mataimakin gwamnan Katsina ya samu zuwa wurin nan. Hakan ta faru ne saboda abinda za a tattauna mai muhimmanci ne. Hakan yasa muka kasa baccin dare."

Ta'addancin Boko Haram ya yi sanadin rayuka 300,000 na yara a arewa maso gabas

A wani labari na daban, sama da yara 300,000 ne suka rasa rayukansu a shekaru 12 da suka gabata sakamakon ta'addancin da ya addabi yankin arewa maso gabas, kiyasin kwanakin nan da UNICEF ta saki ya bayyana.

Wannan na zuwa ne bayan dakarun sojin Najeriya sun bayyana cewa ISWAP ta fara gangamin daukan matasa marasa aikin yi aiki domin tada zaune tsaye, Daily Trust ta ruwaito.

Kiyasin kwanan nan da UNICEF ta saki ya kara da bayyana cewa sama da mutum miliyan daya sun rasa gidajensu a cikin shekaru 12 da suka gabata.

Kara karanta wannan

Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock

Asali: Legit.ng

Online view pixel