Mata mafarauta: A bamu wuka da nama, harsashi ba ya ratsa mu, za mu iya da 'yan bindiga

Mata mafarauta: A bamu wuka da nama, harsashi ba ya ratsa mu, za mu iya da 'yan bindiga

  • Kungiyar mafarautan Najeriya, NHC, reshen jihar Katsina ta yanke shawarar taya gwamnatin jihar yakar ‘yan bindigan da ke a fadin jihar
  • Mataimakiyar kwamanda janar na kungiyar, Hajiya Ummah Dauda ta jagoranci mafarautan zuwa ofishin sakataren gwamnatin
  • Ta ce a matsayinsu na mata mafarauta, harsashi ba ya huda su kuma sun san dajin sosai don haka za su iya yakar miyagun

Katsina - Kungiyar mafarautan Najeriya, NHC, reshen jihar Katsina da ke arewa maso yamma ta yanke shawarar taimaka wa gwamnatin jihar yaki da ta’addanci a fadin jihar.

Hajiya Ummah Dauda, mataimakiyar kwamanda janar na kungiyar, ta jagoranci sauran ‘yan kungiyar zuwa ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Muhammad Inuwa, LIB ta ruwaito.

Mata mafarauta: A bamu wuka da nama, harsashi ba ya ratsa mu, za mu iya da 'yan bindiga
Mata mafarauta: A bamu wuka da nama, harsashi ba ya ratsa mu, za mu iya da 'yan bindiga. Hoto daga lindaikejiblog.com
Asali: UGC

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri

Yayin jawabi a ofishin SAG, ACG Ummah ta bayyana cewa a cikin kungiyar mafarautan da za su iya sadaukar da ran su wurin kawo karshen ta’addanci a jihar.

Kamar yadda ta ce:

“A matsayin mu na mafarauta, mun san daji kwarai don haka mu yafi dacewa a ce mun yaki ‘yan ta’adda a jihar. Da yawan mu muna da tsarin da harsashi ba zai ratsa mu ba. Kuma mun samu horarwa wurin yaki.
“Hakan ya sa na ke rokon gwamnati ta yi wannan tafiyar da mu don kawo karshen ta’addanci a jihar nan.
“Akwai mahauta a kalla 100 a ko wacce karamar hukuma. Kuma akwai kananun hukumomin da sun fi mutane 100 a can.
“Wasu daga cikin mu za su iya kama ‘yan ta’adda kuma su mika su ga jami’an tsaro don yi musu hukunci.
“Don haka muke bukatar gwamnatin jihar nan ta bamu dama don a shirye muke mu kamo su ko a yanzu.”

Kara karanta wannan

Kwana 5 da mutuwar Mailafia, ba bu saƙon ta’aziyya daga Buhari da El-Rufai

Ta bukaci gwamnatin jihar ta sama mu su da ofishi a matsayin daya daga cikin abubuwan da zasu taimaka wurin kammala aikin cikin sauki, LIB ta wallafa.

Ba za mu sakankance bakin haure su mamaye Najeriya ba, Rundunar sojin kasa

A wani labari na daban, kwamandan rundunar hadin guiwa ta Operation Hadin Kai, Maj.-Gen. Christopher Musa, ya ce dakarun sojin Najeriya ba za su bar kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta samu wuri tare da yin kane-kane a Najeriya ba.

Musa ya sanar da hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda ya ce, ISWAP kungiyar ta'addanci ce ta ketare wacce wasu daga kasashen ketaren ke daukar nauyin ta, ta yuwu kuma akwai wasu 'yan Najeriya da ke daukar nauyin ta. Don haka ba ta da wurin zama a kasar nan.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye: Manyan 'yan siyasa 5 da aka kayar a 2019 wadanda ka iya dawowa da karfi a shekarar 2023

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel