Da Ɗuminsa: Jam'iyyar PDP Ta Dakatar Da Jiga-Jiganta Biyu a Borno
- Babban jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, ta dakatar da jiga-jiganta biyu a jihar Borno
- 'Yan jam'iyyar da aka dakatar sun hada da tsohon dan takarar gwamna Mohammed Alkali Imam da tsohon shugaban PDP na jihar Zannah Gaddama Mustapha
- An dakatar da su ne domin suna janyo rabuwar kan a jam'iyyar kamar yadda sakatare Yusuf Mohammed Dikko ya sanar
Jihar Borno - Rikicin cikin gida ya yi sanadin dakatar da manyan 'ya'yan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, biyu a jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.
Wadanda aka dakatar din sun hada da tsohon dan takarar gwamna Mohammed Alkali Imam da tsohon shugaban PDP na jihar Zannah Gaddama Mustapha.

Asali: Facebook
Dalilin dakatar da jiga-jian na PDP?
Daily Trust ta ruwaito cewa Sakataren PDP na jihar Borno, Yusuf Mohammed Dikko, wanda ya sanar da dakatarwar yayin taron 'yan jarida a Maiduguri ya ce wadanda aka dakatar din suna raba kan 'yan jam'iyyar.
Ya ce jiga-jigan biyu duk sun ki amsa tambayoyin da aka yi musu dangane da korafin da shugabannin jam'iyyar na matakin mazabu da kananan hukumomi suka shigar a kansu.
Da aka tuntube shi domin ji ta bakinsa, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na Borno, Mustapha ya ce jam'iyyar bata kafa kwamitin ladabtarwa ba domin yin bincike a kan lamarin.
2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

Kara karanta wannan
Jam’iyyar PDP ta kori tsohon gwamnan Neja Aliyu a matsayin memba na BoT, ta sanar da madadin shi
A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.
Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.
Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.
Asali: Legit.ng