Yan bindiga sun budewa Shanu wuta a jihar Anambra, haka kawai

Yan bindiga sun budewa Shanu wuta a jihar Anambra, haka kawai

  • An kashe Shanun makiyaya a jihar Anambra da sunan dabbaka dokar hana kiwo
  • Wadanda suka budewa Shanun wuta ba jami'an gwamnati bane
  • Mutan gari sun arce yayinda suka ji karar harbin bindiga

Anambra - Wasu yan bindiga sun bindige wasu Shanu dake kiwo a garin Oba, karamar hukumar Idemili-South a jihar Anambra.

Makiyayan dake kiwon Shanun da mutanen gari sun arce yayinda yan bindigan suka fara kashe Shanun, masu idanuwan shaida suka bayyanawa Sahara Reporters.

A cewar wani mai idon shaida, yan bindigan sun kashe Shanun ne da sunan dabbaka dokar hana kiwo a fili a jihar; duk da cewa ba'a kafa dokar hana kiwo a jihar Anambara ba tukun.

Yan majalisar dokokin jihar sun fara tattaunawa kan dokar ranar 22 ga Satumba.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Zaku tuna cewa a ranar 11 ga Mayu, gwamnonin kudancin Najeriya sun yi ittifakin haramta kiwo a fili a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan bindiga sun budewa Shanu wuta a jihar Anambra, haka kawai
Yan bindiga sun budewa Shanu wuta a jihar Anambra, haka kawai
Source: UGC

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

Gwamnan jihar Kaduna ya caccaki gwamnonin kudancin Najeriya kan sabuwar dokar haramta kiwo a fili da suke yi a jihohinsu.

El-Rufa'i a martaninsa kan wannan doka, ya ce ba kafa dokar bane abu mai muhimmanci, aiwatar da dokar ne ba zai yiwu ba.

Zaku tuna cewa kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya karkashin jagorancin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, sun yi ittifakin kafa dokar a yankinsu.

Jihohi irinsu Ondo, Oyo, Lagos, Enugu, Osun, Akwa Ibom da sauransu tuni sun kafa dokar.

Source: Legit.ng

Online view pixel