Bamu kujeran shugaban kasa a 2023 ya zama wajibi, Afenifere ta jaddada bukatar kudu

Bamu kujeran shugaban kasa a 2023 ya zama wajibi, Afenifere ta jaddada bukatar kudu

  • Kungiyar Yarbawa ta jaddada maganar komawar mulki kudu a 2023
  • Afenifere tace kada da kudun da ya yarda a yaudaresu saboda haka aka saba
  • Gwamnonin Kudancin Najeriya sun gana makon da ya gabata

Ondo - Kungiyar kare hakkin yan kabilar Yoruba, Afenifere, ta jaddada bukatar da gwamnonin kudancin Najeriya sukayi na cewa mulki ya koma kudu a shekarar 2023.

Sakataren kungiyar na kasa, Sola Ebiseni, ya bayyana hakan a jawabin da yayi ranar Laraba a garin Akure, jihar Ondo, rahoton Punch.

A jawabin mai take 'Tsarin kama-kama na kujeran shugaban kasa, wajibi ne shugabanci ya koma kudu,' Afenifere tace an dade ana wannan tsari tun da aka dawo demokradiyya.

Yace:

"Shawarar da gwamnonin Kudu suka yi na cewa kujeran shugaban kasa ya koma kudu ba sabon abu bane."

Kara karanta wannan

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

"Ya kamata a duba cewa tun 1999, ana kama-kama tsakanin kudu da Arewa tsakanin Olusegun Obasanjo, Umar Yar’Adua, Goodluck Jonathan da kuma yanzu Shugaba Muhammadu Buhari."

Bamu kujeran shugaban kasa a 2023 ya zama wajibi, Afenifere ta jaddada bukatar kudu
Bamu kujeran shugaban kasa a 2023 ya zama wajibi, Afenifere ta jaddada bukatar kudu Hoto: punchng.com/2023
Asali: UGC

"Wannan shine abinda kowa ya fahimta duk da cewa tun 1999, Arewa ta mamaye kujeran shugabancin kasa a matsayin firai minista, ko na mulkin soja, illa yan shekaru uku da rabi da Olusegun Obasanjo yayi matsayin shugaban mulkin soja."
"Saboda haka rainin hankali ne ace mulki ya koma Arewa bayan shekaru 8 na Buhari don kawai Shugaba Umaru Yar'adua ya mutu bai kara shekaru 8 na Arewa ba."

A karshe, kungiyar tayi kira ga yan jam'iyyu kada su amince da wayau da akeyi na kokarin baiwa kudu kujeran shugabannin jam'iyya. Innama su jajirce kan ganin cewa kujerar shugaban kasa ta koma kudu.

Kara karanta wannan

Rufe iyakokin kasa ya matukar taimaka wa Najeriya, Buhari ga sarauniyar Netherlands

Shugaban kasa a 2023: Kudu ba za ta goyi bayan duk jam’iyyar da ta tsayar da dan arewa ba, in ji gwamnan APC

Gwamnan jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya ce duk wata jam’iyyar siyasa da ta tsayar da dan takarar arewa a matsayin shugaban kasa a 2023 na iya rasa goyon bayan mutanen kudu.

Akeredolu ya bayyana haka ne ranar Juma’a a wata hira da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels.

A yayin da yake magana kan kudurin kungiyar gwamnonin kudancin kasar kan zabukan 2023 da kuma cewa dole ne a bai wa yankin kudu shugabancin kasa, Akeredolu, wanda shi ne shugaban kungiyar, ya ce hakan ta kasance ne domin a yi adalci da daidaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel