Ba za mu tsayar da shugaba daga wata shiyya ba, kwamitin PDP ya magantu kan rabon kujerar shugaban kasa a 2023

Ba za mu tsayar da shugaba daga wata shiyya ba, kwamitin PDP ya magantu kan rabon kujerar shugaban kasa a 2023

  • Kwamitin fito da yadda za ayi rabon kujeru na jam'iyyar PDP a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, ya gana a Enugu, babban birnin jihar Enugu
  • Ifeanyi Ugwuanyi, gwamnan jihar Enugu, wanda kuma shine shugaban kwamitin, ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai jawabi
  • A cewarsa, PDP ita ce jam’iyya guda da za ta iya isar da kyakkyawan shugabanci ga Najeriya

Enugu, Enugu - Kwamitin fito da yadda za ayi rabon kujeru na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 23 ga Satumba, ya ce ba shi da hurumin raba kujerun siyasa irin na shugaban kasa ko mataimakin shugaban Najeriya.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, wanda kuma shine shugaban kwamitin, ya fadi hakan ne a cikin jawabinsa a yayin taron su na farko a gidan gwamnati, Enugu.

Kara karanta wannan

PDP: Yarbawa za su fito da Shugaban Jam’iyya, an ware wa 'Yan Arewa kujera mai tsoka

Ba za mu tsayar da shugaba daga wata shiyya ba, kwamitin PDP ya magantu kan rabon kujerar shugaban kasa a 2023
Ba za mu tsayar da shugaba daga wata shiyya ba, kwamitin PDP ya magantu kan rabon kujerar shugaban kasa a 2023 Hoto: PDP

Legit.ng ta tattaro cewa shugabancin jam'iyyar ne ya kafa kwamitin domin rabawa shiyoyi kujerun PDP na kasa gabanin babban taronta da ake shirin gudanarwa a ranakun 30 da 31 ga watan Oktoba.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kwamitinmu ya tsaya ne kawai ga ofisoshin zartarwa na PDP na kasa wanda za a fafata da su a babban taron PDP na 2021 da aka shirya yi a karshen Oktoba 2021. Ba za mu raba kujerun siyasa irin na shugaban kasa ko mataimakin shugaban Najeriya ba.”

Ya kara da cewa aikin kwamitin zai ba da gudummawa mai yawa “da za su taimaka wa PDP wajen cimma kyawawan manufofin magabatan mu."

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan ya ƙarfafawa membobin kwamitin gwiwa da su kasance masu faɗin gaskiya da buɗe ido a cikin shawarwari da muhawararsu, da nuna daidaito tare da girman aikinsu.

Kara karanta wannan

Aiwatar da dokar hana kiwo a fili abune da ba zai yiwu ba, El-Rufa'i ya caccaki gwamnonin kudu

Ugwuanyi ya ci gaba da cewa:

“An zabi membobi da shugabancin wannan kwamitin a hankali saboda ya kunshi gogaggu, kwararru da fitattun ‘yan Najeriya wadanda ke da burin sake canza PDP don taka rawar ganinta ba wai a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ba amma don gina jam'iyyar da za ta tabbatar da muradin 'yan Najeriya cewa bayan wuya sai dadi."

PDP: Yarbawa za su fito da Shugaban Jam’iyya, an ware wa 'Yan Arewa kujera mai tsoka

A baya mun ji cewa Jam’iyyar PDP na iya kai kujerar shugaban jam’iyya na kasa zuwa yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Jaridar Punch ta fara samun kishin-kishin cewa ‘yan kwamitin da PDP ta kafa domin su fito da yadda za ayi rabon kujeru sun bada shawarwarinsu.

wamitin ya bada shawarar a bar kujerar shugaban jam’iyyar PDP a yankin maso yamma, sai kuma a ware wa ‘Yan Arewa kujerar sakataren jam’iyya.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel