PDP: Yarbawa za su fito da Shugaban Jam’iyya, an ware wa 'Yan Arewa kujera mai tsoka
- Kwamitin Ifeanyi Ugwuanyi ya na aiki a kan yadda za a ware mukamai a PDP
- Ana kishin-kishin cewa wannan karo Bayarabe zai zama shugaban jam’iyyar
- Tun da aka kafa PDP a 1998, 'Yan Kudu maso yamma ba su taba rike kujerar ba
Abuja - Jam’iyyar PDP na iya kai kujerar shugaban jam’iyya na kasa zuwa yankin kudu maso yammacin Najeriya.
Jaridar Punch ta fara samun kishin-kishin cewa ‘yan kwamitin da PDP ta kafa domin su fito da yadda za ayi rabon kujeru sun bada shawarwarinsu.
Kwamitin ya bada shawarar a bar kujerar shugaban jam’iyyar PDP a yankin maso yamma, sai kuma a ware wa ‘Yan Arewa kujerar sakataren jam’iyya.
Shugaban kwamitin, gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi zai jagoranci zaman kwamitin da za ayi yau, ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, 2021.
Takardar da ta shigo hannun jaridar ta nuna cewa kwamitin ya kai kujerar shugaban jam’iyyar zuwa yankin domin ba su taba rike kujerar a tarihi ba.
Su wanene suka rike wannan kujera?
Arewa maso tsakiya sun rike wannan matsayi har sau biyar; Solomon Lar, Barnabas Gemade, Audu Ogbeh, Ahmadu Ali da Abubakar Kawu Baraje.
Daga Arewa maso tsakiya an yi; Dr Bamanga Tukur, Dr Adamu Muazu da Sanata Ali Modu Sheriff wadanda suka yi shugabanci tsakanin 2012 da 2016.
Dr. Haliru Bello da Ahmed Makarfi sune suka rike shugaban PDP na kasa daga Arewa maso yamma.
Vincent Ogbulafor, Okwesilieze Nwodo da Uche Secondus su ne shugabannin da suka fito daga kudu maso kudancin Najeriya tun daga 1999 zuwa yanzu.
A lokacin da Uche Secondus ya zama shugaba, mutane 12 daga kudu maso yammacin Najeriya ake tunani za su gwabza, sai daga baya lissafin ya canza.
Wa zai gaji Prince Uche Secondus?
Ku na da labari cewa tsofaffin shugabannin PDP su na so wanda zai rike Jam’iyyar PDP ya zama mai nagarta kuma wanda babu wanda zai iya juya shi.
A rahoton kun ji cewa kwanan nan ne za a fara tseren wadanda za su samu kujeru a majalisar NWC ta PDP bayan an fatattaki Prince Uche Secondus.
Asali: Legit.ng