Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere

Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere

  • Asibiti ta gudanar da bincike kan gawar budurwa da aka tsinta a motar basarake a Edo
  • Bincike ya nuna cewa budurwar mai shekaru 26 ta mutu ne yayin zubar da juna biyu na wata 8
  • Da farko dai iyalan budurwar suna zargin basaraken duka ya mata har ta kai ga ta ce ga garinku

Edo - Binciken da aka gudanar a kan gawar wata budurwa, Faith Aigbe mai shekaru 26 da aka tsinta a cikin motar basarake na jihar Edo ya nuna cewa ta rasu ne sakamakon juna biyu mai matsala da ta ke dauke da shi, rahoton LIB.

Idan za a iya tunawa dai, an zargi Enogie na Uroho a karamar hukumar Okha na jihar Edo, Iguodala Ogieriakhi da yi wa Faith duka har ya kashe ta bayan tsintar gawarta a motarsa Lexus 330 da ya tsere ya bari a harabar asibiti kamar yadda Legit Hausa ta kawo a baya.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere
Enogie na Uroho, Iguodala Ogieriakhi da tsohuwar budurwarsa, marigayiya Faith Aigbe. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma, basaraken ya musanta zargin, yana mai cewa Faith tana dauke da juna biyu ne na watanni takwas kuma ta rasu ne a lokacin da ta ke kokarin zubar da cikin.

Iyalai da 'yan uwan Aigbe sun musanta cewa 'yarsu na da juna biyu, suna mai cewa Enogie ne ya halaka ta.

Nan take 'yan sanda suka kama Enogie aka tsare shi, yayin da aka jira sakamako daga asibiti kan sanadin mutuwarta.

A ranar Laraba 22 ga watan Satumba ne yan sandan Edo suka fitar da sakamakon dalilin rasuwar marigayiya Aigbe.

'Yan sanda sun ce sakamakon bincike ya nuna ba basaraken ya kashe ta ba

Kakakin yan sanda, Bello Kotongs cikin sanarwar da ya fitar ya ce zubar da jini sakamakon matsala da juna biyun ya samu ne ya yi sanadin mutuwarta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

Sanarwar ta ce:

"Rundunar yan sandan jihar Edo na san sanar da al'umma cewa bincike ya nuna Faith Aigbe ta mutu ne a gidan saurayinta, Enogie na Uroho, Iguodala Ogieriakhi.
"An yi zargin ya halaka budurwarsa mai juna biyu na wata 8. Amma bincike daga asibitin UBTH ya nuna abin da ya kashe ta kamar yadda Dr Wilson Akhiwu ya sanya wa hannu.
"Sakamakon ya nuna zubar jini ne ya yi sanadin mutuwar ta, sakamakon matsalar da juna biyun ya samu. Wannan shine abin da ma'aikatan lafiya suka ce."

Kakakin yan sandan ya kara da cewa hakan na nuna cewa basaraken bai aikata abin da iyalan marigayiyan ke zarginsa ba.

Tashin hankali: An tsinci gawar budurwa cikin motar basarake, ya cika wadonsa da iska

Tunda farko, mun kawo muku rahoton cewa hankulan mutane ya tashi a jiya a harabar asibitin kwararru na jihar Edo da ke Sapele Road a Benin yayin da aka gano gawar wata budurwa rufe cikin wani motar basarake da aka sakayya sunansa kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi na karfafa fashi da makami a arewa, Kungiyar CAN ta yi zargi

Faruwar lamarin ya jefa iyalan budurwar mai shekaru 27, mai suna Faith Aigbe cikin alhini.

Yan uwa da iyalan matar da ta riga mu gidan gaskiya sun taru suna cike da bakin ciki a yayin da gawar ta ke rufe cikin motar kamar yadda rahoton na The Guardian ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel