Kotu ta sanar da ranar yanke hukunci kan shari'ar tsohon sarkin Kano, Sanusi II, da Gwamnatin Kano

Kotu ta sanar da ranar yanke hukunci kan shari'ar tsohon sarkin Kano, Sanusi II, da Gwamnatin Kano

  • Kotun tarayya dake zaman a babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana ranar da zata yanke hukunci kan karar da tsohon sarkin Kano ya shigar
  • Tun bayan sauke shi daga mukamin sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya shigar da gwamnatin kano ƙara da wasu manyan mutane a ƙasar nan
  • Kotun ta bayyana ranar 30 ga watan Nuwanba, a matsayin ranar da zata kawo karshen zaman shari'ar, wato zata yanke hukunci

Abuja - Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ranar Alhamis, ta zaɓi ranar 30 ga watan Nuwanba domin yanke hukunci kan ƙarar da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya shigar.

Tsohon sarkin ya shigar da ƙarar gwamnatin jihar Kano da kuma wasu manyan mutane, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mai shari'a Anwuli Chikere, shine ya bayyana ranar yanke hukuncin bayan sauraron hujjoji daga kowane ɓangare yayin zaman shari'a.

Kara karanta wannan

Mutum 4 Sun Mutu, Yayin da Wata Motar Bas Dauke da Fasinjojin Jihar Kano Ta Zarce Kogi

Tsohon sarkin Kano da Ganduje
Kotu ta bayyana ranar da zata yanke hukunci kan shari'ar tsohon sarkin Kano Sanusi da Gwamna Ganduje Hoto: sunrisenewsng.com
Asali: UGC

Suwa tsohon sarkin ya shigar ƙara gaban kotu?

A ranar 12 ga watan Maris, tsohon sarkin ya maka sufeta janar na yan sanda da kuma darackan hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) kan abinda ya kira, "Tsare shi ba baisa ƙa'ida ba da tauye masa hakki," a gaban ƙotun tarayya Abuja.

Sauran waɗanda ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/357/2020 ta ƙunsa, sun haɗa da Antoni janar na jihar Kano da kuma ministan shari'a na ƙasa.

Shin me karar tsohon sarkin ta ƙunsa?

A cikin ƙarar da ya shigar ta hannun tawagar lauyoyinsa, Sanusi II, ya bukaci kotu ta bada umarnin a sake shi daga tsare shi da aka yi kuma a maida masa da yancinsa.

Legit.ng Hausa ta gano cewa an tsare Muhammad Sanusi II a garin Awe dake jihar Nasarawa, bayan sauke shi daga karagar mulki ta sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan Bindigan dake tserowa daga luguden wutan Sojoji a Katsina da Zamfara sun fara shiga Kano

Alkalin dake jagorantar shari'ar, Anwuli Chikere, ya bada umarnin sakin tsohon sarkin tun a wancan lokacin.

Sai dai duk da samun wannan nasara ta sakinsa da aka yi, Kotu ta cigaba da sauraron ƙarar, kuma har yanzun bata yanke hukunci ba.

A wani labarin kuma Gwamnatin Zulum ta fara shiri na musamman ga mayakan Boko Haram da suka mika wuya

Gwamnatin jihar Borno ta kaddamar da fara shirin canza yan ƙungiyar Boko Haram da suka miƙa wuya

Kwamishinan labaru, Abba Jato, yace ya zama wajibi a karbi masu mika wuyan domin mafi yawansu mata ne da ƙananan yara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262